IQNA

Yahudawa Masu Tsaurar Ra’ayi Sun Baka Wa Ni Masallaci Wuta

19:36 - February 25, 2015
Lambar Labari: 2897127
Bangaren kasa da kasa, Wasu yahudawa sahyuniya 'yan kaka gida masu tsatsauran ra'ayi sun banka ma wani masallaci wuta da ke yankin gabar yamma da kogin Jordan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, Wasu yahudawa sahyuniya 'yan kaka gida masu tsatsauran ra'ayi dauke da bindigogi sun banka ma wani masallaci wuta a kauyen Al-jab’a a kudancin garin bait Laham da ke yankin gabar yamma da kogin Jordan, inda suka kone shi kurmus. 
Jami'an gwamnatin kwarya-kwarya cin gishin kai ta Palastinawa sun ce yahudawan sun killace masallacin ne suna dauke da makamai, ta yadda Palastinawan da ke wurin ba za su iya tunkararsu ba, inda suka banka wuta kan masallacin tare da cikakkiyar masaniya daga jami'an tsaron Isra'ila, wanda kuma ba shi ne karon farko da suke yin hakan ba a wannan kauye, inda a cikin  shekara ta dubu biyu da goma sha biyu sun kone wani masallaci a wurin.

A cikin 'yan kwanakin nan dai yahudawan sahyuniya suna kai farmaki kan yankunan palastinawa da ke gabacin birnin Qods da kuma gabar yamma da kogin Jordan, inda suke kone masallatai da kuma makarantu gami da kaddarorin palastinawa, kamar yadda jami'an tsaron yahudawan na Isra'ila suke bi gida-gida suna kame matasa.

Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ce da kanta take bayar da kariya ta tsaro ga yahudawan da suke aikata wannan mummmuna aiki kan palastinawa, da kuma gidajensu da wuraren ibadarsu.

2894853

Abubuwan Da Ya Shafa: Palestinu
captcha