IQNA

Zanga-Zangar Musulmin Austria A Rashin Amincewa Da Dokokin Takura Musu

19:39 - February 25, 2015
Lambar Labari: 2897128
Bangaren kasa da kasa, daruruwan musulmin kasar Austria sun gudanar da gangami a gaban majalisar dokokin kasar domin nuna rashin amincewa da sabbin dokokin kasar da ke nufin takura musu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Almisriyun cewa, a jiya kimanin musulmi 250 ne a kasar Austria sun gudanar da zanga-zanga a gaban majalisar dokokin kasar domin nuna rashin amincewa da sabbin dokokin kasar da ke nufin takura musu a kan harkokin addininsu.

A cikin wani bayani da masu zanga-zangar suka fitar wanda aka aike wa shugaban mjaliasar dokokin kasar da shi, sun nuna rashin gamsuwarsu da irin matakan da ake shirin dauka na samar da sabbin dokoki da za su takura musu a kan harkokinsu na addini, domin kuwa su ma ‘yan kasa ne kamar kowa suna da dukkanin hakkokinsu da ya zama dole gwamnati ta kiyaye.

Sabbin dokokin na kasar Austria na shirin hana musulmi gudanar da lamurransu cikin ‘yanci, wanda hakan baya rasa nasaba da abubuwan da suke faruwa a cikin lokutan nan musamman ma kai hare-haren ta’addanci da wasu ke yi da suna  addinin muslunci a cikin kasashen turai da ma wasu yankuna, lamarin da ake firgita sauran mabiya wasu addinai da shi Kenan dangane da musulunci.

Majalisar dokokin ta Austria ta ce za ta yi nazari kan korafin da musulmin suka gabatar, kuma za a sassauta wasu daga cikin dokokin domin baiwa musulmin hakkokinsu, daga ciki kuwa har da basu damar yin yanka, da kuma ba su damar yin tarukansu a lokutansu na addini musamman ranaku na musamman ga musulmi da suka hada da idi da sauransu.

Idan aka amince da hakan za a mika ma shugaban kasa domin saka hannu, ta yadda za a baiwa musulmi damar gudanar da harkokinsu na addini ba tare da tsangwama ba.

2894876

Abubuwan Da Ya Shafa: austria
captcha