IQNA

Za A Bude wata Sabuwar Tashar Radio Ta Kur'ani A Kasar Masar

23:03 - March 02, 2015
Lambar Labari: 2918920
Bangaren kasa da kasa, a yau ne za a bude wata sabuwar tashar radio ta karatun kur'ani mai tsarki a garin Santa da ke yammacin kasar Masar da nufin watsa shirinsa a cikin kasashen arewacin Afirka da kuma nahiyar turai.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Almisral youm cewa, Muhamamd Mukhtar Juma'a ministan harkokin addini na Masar yana cewa yau ne za a bude wata sabuwar tashar radio mai suna Attaqwiyyah ta karatun kur'ani mai tsarki wadda zata rika watsa shirinta domin amfanin cikin gida da kashen ketare.
Mohammad Mukhtar Juma'a wanda shi ne zai wakilci firayi ministan kasar Ibrahim mahlab ya bayyana cewa wannan taro zai samu halartar wasu daga cikin manyan jami'an gwamnati, da suka hada hard a shugaban hukumar radio da talabijin na kasar Majdi Amin, da kuma wakilan wasu cibiyoyin musulmi daga nahiyar turai.
Ya kara da cewa wannan shiri zai samu karbuwa matuka da kuma mafanawarwa ga mabiya addinin muslunci da suke bukatar kara samun ilimin kur'ani mai tsarki, na karatu da kuma sain hakikanin ma'anoninsa.

2917579

Abubuwan Da Ya Shafa: radio
captcha