Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, hadakar limaman masallatan kasar Faransa na shirin gudanar da wani taro na wayar da kai dangane da addinin muslunci da yazo da shi wanda za a yi masallacin Libiyun.
Su ma a nasu bangaren mahukuntan kasar Faransa za su yi dubi dangane da wani korafi da mabiya addinin muslunci na kasar suka gabatar bisa la'akari da muhimmaiyar rawar da suke takawa wajen kawo zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al'ummomin kasar.
A cikin watan janairun da ya gabata an samu wasu masu tsattsauran ra'ayi a cikin kasar Faransa suna kai hari kan musulmin kasar, yayin da kuma acikin shekara ta dubu biyu da goma sha huhu an samu irin wannan yanayi marassa kyau, amma cewar ministan harkokin cikin gida na kasar suna daukar dukaknin matakan da suka dace domin kare rayukan musulmi da kuma dukiyoyinsu.
Ya kara da cewa mabiya addinin muslunci sun nuna dattijantaka matuka kana bin day a faru, domin kuwa sun nuna rashin jin dadinsu dangane da hare-haren da aka kai a kasar, a kan babu dalilin da zai sanya su kuma a dauke su matsayin abokan gaba, musulmin faransa daidai suke da kowane dan kasa, suna da dukkanin hakkokinsu na yan kasa ba tare da banbanci ba.
Masu kula da harkokin babban masallacin na Libiyun sun ce shirin zai mayar da hankali ne wajen wajen fadakar da su kansu musulmi kan hakikanin koyarwar musulunci ta zaman lafiya, maimakon bin akidun tayar da hankali da sunan jihadi ko abin da ya yi kama da hakan.
Haka nan su ma mutanen da ba musulmi za a nuna musu cewa shi addinin muslunci y azo kamar yadda aka safkar da shi domin ya zama rahma ga taliai baki daya, kuma masu ta’addanci bas u wakiltarsa.
2920078