IQNA

Musulmin Austria Na Aiki Tare Da Gwamnati Domin Yaki Da Tsatsauran Ra'ayi

22:24 - March 04, 2015
Lambar Labari: 2928898
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci a kasar Austria suna baiwa gwamnatin kasar hadin kai wajen shiga kafar wando daya da masu tsatsauran ra'ayi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na On Islam cewa, Da dama daga cikin mabiya addinin muslunci a kasar Austria suna baiwa gwamnatin kasar hadin kai wajen shiga kafar wando daya da masu tsatsauran ra'ayi da ake samu tsakanin musulmin.
Haka na wakana ne ta hanayr bude wani layi wanda ake tuntuba domin bayyana wadanda suka kamu da wannan matsala ta ra'ayin ta'addanci,a  cikin wanann tsakanin kimanin iyalai 200 suka kira layin domin bayar da bayani.
Matasa 130 ne daga kasar ta Austria suka tafi Syria domin yaki, amma zuwa cikin watan janairu adadin ya kai 190, amma daga bisani kuma wasu kimani 70 sun dawo kasar, inda suka nuna sun bar wannan hanya ta ta'addanci.
A makon day a gabata ne wasu musulmi suka jerin gwano domin nuna rashin amincewa da wasu matakai na takurawa, cikin wani bayani da suka fitar wanda aka aike wa shugaban mjaliasar dokokin kasar da shi, sun nuna rashin gamsuwarsu da irin matakan da ake shirin dauka na samar da sabbin dokoki da za su takura musu a kan harkokinsu na addini.
Domin kuwa su ma ‘yan kasa ne kamar kowa suna da dukkanin hakkokinsu da ya zama dole gwamnati ta kiyaye, sabbin dokokin na kasar Austria na shirin hana musulmi gudanar da lamurransu cikin ‘yanci, wanda hakan baya rasa nasaba da abubuwan da suke faruwa a cikin lokutan nan musamman ma kai hare-haren ta’addanci da wasu ke yi da suna  addinin muslunci.
Ita majalisar dokokin ta Austria ta ce za ta yi nazari kan korafin da musulmin suka gabatar, kuma za a sassauta wasu daga cikin dokokin domin baiwa musulmin hakkokinsu, daga ciki kuwa har da basu damar yin yanka, da kuma ba su damar yin tarukansu a lokutansu na addini musamman ranaku na musamman ga musulmi da suka hada da idi da amkamantansu.
2924640

Abubuwan Da Ya Shafa: austria
captcha