Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-alam cewa, kungiuyar ‘yan ta’addar dai ta yi amfani da motocin buldoza wajen rushe tsohon birnin wanda ya ke a karkashin wuraren tarihin dauri na Iraki,kamar yadda majiyar gwamnatin kasar ta ambata.
Majiyar ta ci gaba da cewa da tsakiyar ranar jiya alhamis ne dai aka fara rushe birnin. Birnin Lamarudu dai an gina shi ne shekaru dubu daya da dari uku kafin haihuwar ananbi Isa amincin Allah ya tabbata a gare shi a wurin da ya ke da nisan kilo mita 30 daga birnin Mousel.
Ana jin tsoron cewa ‘yan kungiyar ta Da’ish, za su rushe wani tsoron birnin na Hatra da nan ne cibiyar yankin Nineveh da ke da tarihin fiye da shekaru dubu biyu.
Kusan makwanni biyu kenan da ‘yan da’ish su ka rushe kayan tarihi da su ke cikin gidan aje kayan mutaned da a cikin birnin Mousel.