IQNA

An karayata Labarin Tababtar Da Hukuncin Kisa Kan Sheikh Namir

19:40 - March 06, 2015
Lambar Labari: 2936147
Bangaren kasa da kasa, an karyata labarin amincewa da hukuncin kisa kan malamin shi'a na kasar Saudiyyah Sheikh Baqer Namir.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na na Masdark News cews, Sadeq Aljiran lauya mai kare Sheikh Namir da kuma dan uwansa Mohammad Namir sun karyata labarin amincewa da hukuncin kisa kan malamin.
Malamin dan shekaru hamsin da haihuwa ya sahara a kasar Saudiyya da ma kasashen larabawa, wajen gwagwarmayarsa ta kare hakkokin mutane da ake zalunta, da kuma bude cibiyoyin ilimi da wayar da kan al'umma kan harkoki na zamantakewa da kuma siyasa a addinance, wannan ya sanya shi ya samu karbuwa a wajen mutane da dama a kasar ta Saudiyya, mabiya mazhabar shi'a da ma wadanda ba su ba, musamman talakawa daga cikin mutanen kasar, sakamakon tunkarar sarakunan kasar da yake yi tare da fada musu gaskiya, abin da sauran malaman kasar ba za su iya yi ba.
A cikin watan Agustan shekara ta dubu biyu da takwas gwamnatin Saudiyya ta kafa masa takunkumin na hana shi gabatar da laccoci ko fitar da makaloli da sauran rubuce-rubuce da ya saba yi, na addini ne ko na siyasa ko kuma na zamantakewa, tare da sanya idon  jami'an tsaro a kansa.
Haka nan kuma a cikin shekara ta dubu biyu das ha daya al'ummomi a yankunan qatif da Ihsa da kuma Awamiyyah da ma sauran yankunan gabacin Saudiyya wanda akasarin mazauna wadannan yankuna mabiya mazhabar shi'a ne, kuma a nan ne dukkanin arzikin danyen manfetur da iskar gas da kasar Saudiyya take da shi yake, suka fito suna nuna rashin amincewarsu da salon mulkin mulukiya na kasar, tare da neman a saki dubban fursunonin siyasa da mahukuntan kasar suke tsare da su.
Sun kuma nemi da a yi adalci wajen rabon arzikin kasar musamamn ma ganin cewa arzikin manfetur da iskar gas da kasar Saudiyya ta dogara da shi daga yankinsu ake fitar da shi, amma mahukuntan kasar sun yi amfani da karfi wajen murkushe su tare da kashe adadi mai yawa da kuma kame wasu dubbai daga cikinsu, wanda hakan ya sanya Sheikh Namir ya fito ya soki wannan mataki da mahukuntan kasar suke dauka kan fararen hula masu zanga-zangar lumana domin neman hakkokinsu da aka haramta musu.
2935054

Abubuwan Da Ya Shafa: sheikh Namir
captcha