Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Sadal Balad cewa, sheikh Ahamd Tayyib a wani jawabi da ya gabatar ta tashar latabijin din kasar ga mutanan Japan, ya jaddada wajibcin yaki da akidun wuce gona da iri wadanda suke bata fuskar addinin musulunci a kasashen duniya baki daya.
Sheikh Tayyeeb ya ce Jami'ar Al-Azhar zata yi yaki da wadannan mummunan ikidu ta hanyar yada akidun musulunci na gaskiya da kuma bude fagen muhawara da jawabai don kushe dukkan akidu masu munana fuskar addinin musulunci a kasashen larabawa, ya jaddada muhimmancin Jami'ar Al-Azhar a matsayinta na cibiyar ta yada addinin musulunci, wajen yakar yan ta'adda da kuma mummunan akidun da wasu ke dangantasu da addinin musuluni.
Jami'ar Al'azhar ta kasar Masar ta ce mayakan da'esh ko Isis su fita daga cikin musulinci. A wata fatawa da ta fitar jiya, jami'ar Al'azhar ta ce wajibi mahumta su yaki kungiyar ta 'adancin nan ta ISIS domin Al'umma duniya ta huta da sharinsu. fatawar ta ce kungiyar ISIS ba ta da wani banbaci da.
Yayin da suke aibata aiyukan kungiyar ISIS, maliman Al'azhar sun bayyana cewa kungiyar ta ISIS na yaudarar matasan musulmi da yin jihadi da sunan musulnci, yayin da aiyukan kungiyar yayin hanun riga da Addinin Islama.
Manufar kafa wannan kungiyar bata sunan musulmi da musulinci sannan maliman na Azhar sun bukaci Al'ummar musulmi da su yi taka tsan-tsan wajen daukar irin wannan mumunar akida tare da neman maluma da su ci gaba da wayewa Al'ummar kai dangane da wannan gurbataciyar Akida.
Daga karshe Shehu Azhar Ahmad Attayib ya bayyana kungiyar ta ISIS a matsayin wani makamin kasashen yamma domin kafa sabuwar gabas ta tsakiya kamar yadda suka bayyana a baya, sannan ya ce manufar su rarraba duniyar musulmi.