Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Islam – France.org cewa, a jiya ne aka gudanar da gagarumin gangami domin nuna rashin amincewa da kiyayya da muslunci da wasu suke yi a kasar wanda ya yi hannun riga da dokokin kasar baki daya.
Bayanin ay ci gaba da cewa wannan gangami ya samu halartar dubban mutane da suka cika manyan titunan birnin babban birnin kasar suna rera taken neman a daukai dukkanin atakan da suka dace domin kare hakkokin musulmi a kasar, tare da kuma shiga kafar wando daya da maso neman haddasa fitina ta hanyar tsokanar musulmi.
Tun bayan da aka kai harin birnina kwanakin baya, ake ta samun karuwar masu adawa da muslunci suna gudanar da taruka da kuma gangamia kasar da ma wasu kasashen yammacin turai domin nuna tsananin kiyayrsu da addinin muslunci, tare da tsokanar musulmia duk inda suke, amkma dai malamai dam asana suna ci gaba da gudanar da taruka na wayar da kai ga mutane.
yanzu kimanin kasashe biyar ne aka gudanar da wanann zanga-zanga ta kin muslunci, amma kuma ana samun wasu daga cikin musulmi da ma wadanda ba musulmi ba suna nuna rashin amincewarsu da hakan, inda suma sukan gudanar da nasu gangamin.