Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar ABC News cewa, manufar wannan shiri ne ya wayar da kan mutanen da ba musulmi ba akasar domin suna mummunar fahimta kana abin da ake gaya musu kan musulunci.
Wasim Radhawi shugaban kwalejin bincike kan addinin musulunci ya sheda cewa, sun fara aiwatar da wannan shiri ne tun a cikin makonni da suka gabata domin tabbatar da cewa sun wayar da kan mutane da ake rudar da su kan muslunci, amma kuma alhali abin da ya kamata su sani shi ne musulmi za su ne za su sanmar da su addininsu.
Ya ci gaba da cewa ko shakka babu wannan shiri zai bababn tasiri wajen fadakar da mutane tare da sanar da su hakikanin muslunci da kuma koyarwrsa ta asali.
Dangane da masu bata sunan muslunci kuwa, ya bayyana cewa ya zama wajibi su san cewa abin da suke yi bas hi da wata alaka da musulunci, kuma suna yi wa makiya muslunci aiki ne da nufin dushe hasken wannan addini mai tsarki.