IQNA

A Canja Kyamar Musulunci Da Bayyana Mulsunci Na Hakika Ga Al’ummomi

22:36 - March 12, 2015
Lambar Labari: 2971471
Bangaren siyasa, ya zama dole a mu canja barazaran da ake yi ta kyamar musulmi da bayyana musulunci na gaskiya, mu bayyana banbancinsa da akidar watsi da addini, rahamarsa ga raunana, jihadinsa a kan masu girman kai, ta haka za mu hana makiya samun damar kawar da hankulan duniya daga muslunci na gaskiya.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jagora cewa, a safiyar yau Alhamis ne Jagoron juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da shugaba da membobin majalisar kwararru ta jagoranci ta Iran inda ya bayyana tabbatuwa da kuma aiwatar da ‘Musulunci gaba daya' a matsayin wata bukata ta Ubangiji Madaukakin Sarki sannan kuma babbar manufar tsarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da wajibcin gabatar da Musulunci na hakika don fada da kokarin da ma'abota girman kai suke yi na yada tsoro da kiyayya da Musuluncin a tsakanin al'ummomin duniya, Jagoran cewa ya yi: Wajibi ne a zurfafa tunani yayin dubi da binciken dalilai da hanyoyin magance kalubalen da ake fuskanta, sannan kuma a yi amfani da hankali wajen magance su.
Haka nan kuma yayin da yake magana kan zaben Ayatullah Muhammad Yazdi a matsayin sabon shugaban majalisar kwararru ta jagorancin ta Iran, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana wannan zaben a matsayin zaben da ya dace yana mai cewa: Wannan zaben da aka gudanar da shi ba tare da wani kace nace ba, lalle yana iya zama abin koyi ga sauran cibiyoyin gwamnati.
A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayi ishara da ayoyi daban-daban na Alkur'ani mai girma wajen tabbatar da wajibcin kula da kuma riko da dukkanin koyarwar Musulunci yana mai cewa: A koyarwar Musulunci, babu wani abu mai suna riko da wani bangare, wajibi ne manufa ta kasance ita ce tabbatar da dukkanin bangarori na Musulunci, sannan kuma a zage dantse wajen tabbatar da hakan.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da wajibcin kiyayewa da kuma karfafa dukkanin bangarorin Musulunci cikin rayuwa, Ayatullah Khamenei cewa yayi: Wajibi ne a sanya kiyaye ‘tafarkin Musulunci', ya zamanto shi ne manufar da aka sa a gaba, haka nan kuma a gudanar da tsare-tsare masu kyau wajen cimma wannan manufar kamar yadda kuma wajibi ne kowa da kowa yayi riko da wannan tafarkin.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana ma'abota girman kan duniya a matsayin manyan masu kafar ungulu ga kokarin tabbatar da Musulunci na hakika yana mai cewa: Irin yadda cibiyoyin farfaganda da siyasar sahyoniyawa suke yada kyamar Musulunci da tsorotar da mutane kansa, wata alama ce da take nuni da irin tsaka mai wuya da kuma tsananin damuwar da suke ciki dangane da yadda haramtattun manufofinsu suke ta faduwa (daya bayan daya).
Haka nan kuma yayin da yake magana kan maganganun wasu daga cikin makiyan gwamnatin Musulunci ta Iran da suke cewa su din nan ba suna so ne su sauya tsarin Jamhuriyar Musulunci ba face dai irin halaye da dabi'unta ne suke son sauyawa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: Sauya halayen gwamnatin Musulunci, yana nufin al'ummar Iran su yi watsi da abin da suke bukata wajen ciyar da tafarkin ci gabansu da suka rika sannan kuma su yi kasa a gwiwa a kokarin da suke yin a aiwatar da Musulunci. A hakikanin gaskiya, hakan shi ne dai wannan kokari da suke yi na ganin bayan wannan tsari da kuma irin riko da Musulunci da al'ummar Iran suka yi, sai dai a wannan karon ta wata hanyar ta daban.
Jagoran ya ci gaba da cewa: A hakikanin gaskiya sanya tsoron Musulunci cikin zukatan al'ummomi (da ma'abota girman kai suke yi) wata alama ce dake nuni da damuwa da kuma halin tsoron da ma'abota girman kan suke ciki dangane da Musuluncin da ke tsara rayuwar al'umma da siyasarsu ta rayuwa wanda a halin yanzu al'ummar Iran, ta hanyar juyin juya halinsu, suke jagorantarsa da kuma tabbatar da karfinsa.
Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar ana iya mai da irin wannan tsoro da adawar da ake nuna wa Musulunci ya zamanto wata dama ta ci gaba. Jagoran ya ce: Irin kokari ba kama hannnun yaro da ake yi wajen sanya tsoron Musulunci cikin zukatan al'ummomi da matasa, ya haifar da alamar tambaya cikin zukatan al'ummomin na cewa mene ne dalilin irin wannan bakar farfaganda da ake yadawa kan Musulunci?
Jagoran juyin juya halin Musuluncin dai ya ce ingantacciyar amsar wannan tambayar dai tana cikin gabatarwa da Musulunci na hakika ga al'ummomin duniyan ne, don haka sai yayi kira da cewa: Wajibi ne kowa ya ba da tasa gudummawar a wannan bangaren.
Yayin da yake bayanin siffofin wannan Musuluncin na hakika, Jagoran cewa yayi: Gabatar da Musulunci mai goyon bayan wadanda aka zalunta da kuma adawa da azzalumai, hakan wani lamari ne da zai janyo hankulan matasa a duk inda suke a duniya da kuma fahimtar da su da cewa Musulunci dai yana da tsari a aikace na goyon bayan wadanda ake zalunta kuma marasa kariya.
Ayatullah Khamenei ya bayyana Musulunci mai goyon bayan amfani da hankali da kuma fada da wauta, koma baya da camfe-camfe a matsayin wata siffar ta daban ta Musulunci na hakika. Daga nan sai ya ce: Wajibi ne mu gabatar wa duniya da Musulunci mai kishin al'umma, sabanin Musulunci dan ba ruwanmu, da Musulunci da ke tsara rayuwar mutane, sabanin Musulunci da babu ruwansa da addini da kuma Musulunci mai tausayin rauna da kuma fada da ma'abota girman kai. Ta hakan ne za mu iya mai da wannan shiri na sanya tsoro da gabar Musulunci cikin zukata da makiya suke yi ya zamanto aiki baban giwa kana kuma wata dama ta janyo hankula da zukatan al'ummomi zuwa ga Musulunci na hakika.
A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayi ishara da rikicin da ke tsakanin Iran da Amurka da wasu kasashen Turai ciki kuwa har da batun shirin nukiliyan Iran inda ya ce: Wajibi ne a yi amfani da zurfin tunani wajen dubi cikin wadannan matsaloli da ake da su, sannan kuma a yi amfani da hakan wajen gano mafita da hanyar da ta dace wajen magance su.
Jagoran yayi ishara da rikicin da ya kunno kai sakamakon takunkumin da aka sanya wa Iran a matsayin daya daga cikin misalan irin wadannan rikici da kalubalen inda ya ce: Bincike da kyau zai tabbatar mana da cewa dalilin cutuwar da muka yi da wadannan takunkumin ya samo asali ne saboda dogaro da man fetur da kasar nan ta yi da kuma rashin shigo da mutane cikin harkokin tattalin arziki na kasa.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Idan da ba mu damfara tattalin arzikin kasar nan da kuma rayuwar mutane ga kudin shigar man fetur ba, sannan kuma muka nesanci kura-kuran da aka yi farko-farkon juyin juya halin Musulunci na jingina komai ga gwamnati, da kuwa mutane sun shigo cikin harkokin tattalin arziki, shin makiya za su sami damar yi mana irin wannan cutarwar da suka yi mana ta hanyar sanya takunkumin man fetur da kuma cibiyoyin gwamnati?
Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Idan har muka kalli lamurra da wannan mahangar da kuma magance su, to kuwa za a magance matsaloli, sannan kuma ba za mu dinga kallon makiya ba.
Yayin da yake magana kan amfani da sakamako mai kyau na wannan mahangar, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da tattaunawar nukiliya da ake yi, inda ya ce: A hakikanin gaskiya tawagar da mai girma shugaban kasa ya zaba wajen tattaunawar suna gudanar da ayyukansu da kyau da kuma nuna kishi, sannan kuma suna kokari ainun, to amma duk da kasantuwar wadannan ‘yan'uwa masu kishin, lalle ni dai hankalina bai kwanta ba. Don kuwa daya bangaren da ake tattaunawa da shi din mayaudari ne. Yana biyowa ta bayan fage yana cutarwa.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da kuskuren da wasu suke yi na cewa mai karfi ba ya bukatar yin yaudara, Jagoran cewa yayi: Wasu suna tunanin cewa Amurka da irin wannan karfi na siyasa da tattalin arziki da soji da take da shi, ba ta bukatar amfani da yaudara. To amma sabanin hakan, Amurkawa suna bukatar amfani da yaudara. A halin yanzu ma abin da suke yi kenan. To a hakikanin gaskiya hakan shi ne abin damuwar.
Jagoran dai yayi kiran da a sanya ido kan wannan yaudara ta Amurkawan yana mai cewa: Amurkawa dai a koda yaushe sukan sauya maganganunsu da nuna tsauri a duk lokacin da aka kusato wa'adin da aka tsara na wannan tattaunawar, don su cimma manufofinsu. Don haka wajibi ne a kula da wannan yaudara da dabarar.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da maganganun maras mafadi da Amurkawan suke yi cikin makonni da ranakun baya-bayan nan, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Wani dan wasan kwaikwayo Basahayoniye (Netanyahu) da yayi magana a can, duk da kokarin da jami'an Amurkan suka yi wajen nesanta kansu da hakan, sun fadi wasu maganganu wadanda a cikin maganganun ma sun tuhumci Iran da goyon bayan ayyukan ta'addanci, wanda a hakikanin gaskiya magana ce abar dariya.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Amurkawa da kawayensu na yankin nan, su ne suka kirkiro mafi muni da rashin tausayin ‘yan ta'addan, wato ‘yan kungiyar ISIS da makamantansu, sannan kuma suna ci gaba da goyon bayansu. Amma kuma suna damfara hakan ga al'ummar Iran da gwamnatin Jamhuriyar Musulunci.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da irin goyon baya a fili da gwamnatin Amurka take ba wa haramtacciyar gwamnatin Sahyoniyawa inda ya ce: A fili gwamnatin Amurka take goyon bayan gwamnatin da a fili kuma a hukumance take bayyanar da ayyukan ta'addancin da take yi, amma kuma tana tuhumar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da goyon bayan ayyukan ta'addanci.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana wasikar baya-bayan nan da wasu ‘yan majalisar Amurka suka aiko wa Iran da cewa wata alama ce da take nuni da rugujewar kyawawan halaye na siyasa da gwamnatin Amurka take fuskanta inda ya ce: Dukkanin kasashen duniya, bisa tsarin da aka tafi a kai a duniya, sukan girmama yarjejeniyoyin da gwamnatin da ta gabata ta kulla bayan zuwan wata sabuwar gwamnatin. To amma a fili wadannan ‘yan majalisa na Amurka suka sanar da cewa za su yi watsi da yarjejeniyar da wannan gwamnatin ta kulla bayan tafiyarta. Shin wannan ba rugujewar kyawawan halaye na siyasa da gwamnatin Amurkan take fuskanta ba ne?
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Jami'an Jamhuriyar Musulunci dai sun san me suke yi, sun san yadda za su yi koda kuwa an cimma yarjejeniyar ta yadda daga baya gwamnatin Amurkan ba za ta iya cin kafafunsu ba.
Daga karshe Ayatullah Khamenei ya bayyana tsohon shugaban majalisar kwararru ta jagorancin marigayi Ayatullah Mahdawi Kani a matsayin malami kuma mai aiki da ilimin da yake da shi kana kuma babban mujahidin, don haka sai ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya yi masa rahama.
Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musuluncin dai, sai da shugaban majalisar kwararru ta jagorancin ta Iran Ayatullah Muhammad Yazdi ya gabatar da rahoto kan zaman majalisar karo na 17 da aka gudanar.
Ayatullah Yazdi ya bayyana dubi cikin batun tattaunawar nukiliya da sauran batutuwa na cikin gida, jaddawa kan wajibcin tabbatar da siyasar tattalin arzikin dogaro da kai da kuma nesantar riko da take da maganganu na fatar baki, haka nan kuma da gabatar da rahoto kan mahangar Musulunci dangane da lamurran da suke faruwa a duniya musamman kan batun irin tsoron Musulunci da ake sanya a zukatan al'ummomin kasashen yammaci, a matsayin wasu daga cikin batutuwan da ‘yan majalisar suka tattauna kansu tsawon kwanaki biyu na taron nasu.

2968385

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha