IQNA

22:40 - March 12, 2015
Lambar Labari: 2971473
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci a kasar Kenya a birnin Kismao sun nuna rashin amincewarsu da hukuncin kotun kolin kasar da ke hana musulmi mata saka hijabi a makarntu.

Kmafanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na The Star cewa, Fraida Salim mamba a kwamitin kare hakkokin musulmi a kasar Kenya ta bayyana cewa ba za su taba amincewa da wannan hukunci ba, domin kuwa ya saba dukkanin dokokin dake cikin kundin tsarin mulkin kasar.
Ta ci gaba da cewa y azo a cikin ayoyin doka da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar cewa, dukkanin dan kasa yana hakkin ya y addinin da yake so, kuma babu abin da ya hana musulmi su yi amfani da koyarsu ta fuskar sa tufafi ko abin da ya yi kama da hakan a cikin dokokin da ke cikinkundin tsarin mulkin kasar.
Babban alkain kotun kolin kasar ta Kenya Harun Magui n4e ya sanar da wannan hukunci na kotun kolin kasa kan cewa, mata musulmi bas u da hakkin su amfani da hijabi a cikin makarantu, kuma wannan zai shafi dukkanin makarantun kasar ne ba tare da kebance wani bangare ba.
Wannan hukunci dai na ci gaba da fuskntar suka daga bangarori na kare hakkin bil adama  aciki da wajen kasar ta Kenya, da ke nuna cewa lalai hakan tamkar nuna wariya ne ga mabiya addinin muslunci.
Wata majami’a ce dai ta gabatr da kara kan cewa saka hijabin muslunci da dalibai mata suke yi a makarantun kasar yana jawo matsaloli tsakanin dalibai.
2963012

Abubuwan Da Ya Shafa: Kenya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: