IQNA

Ministan Kula Da Harkokin Addini A Aljeriya Ya Ce Babu Tsatsauran Ra’ayi A Addini

22:42 - March 12, 2015
Lambar Labari: 2971475
Bangaren kasa da kasa, Muhammad Isa minister mai kula da harkokin addini a kasar Aljeriya ya bayyana cewa addinin muslunci bai amince da tsatsauran ra’ayi ba.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-watan cewa, a jiya Muhammad Isa minister mai kula da harkokin addini a kasar Aljeriya ya bayyana cewa addinin muslunci bai amince da tsatsauran ra’ayi ba a cikin lamurransa.
Ministan ya bayyana hakan ne a wajen wani taro da aka bude kan fahimtar juna a tsakanin bangarori na mabiya addinai a kasar, tare da yin kira ga masu karktacciyar fahimta kan addinin muslunci da su fahimci cewa shi addini ne na rahma da jin kai.
Dangan ed amasu bata addinin muslinci suna danganta shi da ayykan ta’addanci kuwa, ministan ya yi gare su da su san cewa babu wani abu ta’addanci a cikin addinin musulunci, kuma yana da kyau su fahimci muslunci ta hanyar koyarwarsa, mai makon abin da aka fada musu.
Daga karshe ya yi kiran cewa ya zama wajibi ga dukaknin bangarori na addinin muslunci musamman ma dai malamai da su mike kai da fata wajen fadakar da matasa da suke da rauni wajen fahimtar hakikanin addini kuma ake saurin yaudararsu, domin su zama cikin fadaka da sahihin tunani kan muslunci.
2964139

Abubuwan Da Ya Shafa: algeria
captcha