Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na RQC cewa, wanann horo zai gudana ne a ranakun 3 da kuma 4 na watan Ramadan mai alfarma, haka nan kuma a ranakun 10 da kuma 11 na wannan wata.
Taron zai samu halatatr manyan malamai masana kan ilmomin kr’ani daga jami’oi da suka suka hada da kwalejin ilmomin muslunci da ke jami’ar Cambrige da wasu sauran jami’oi na kasar, inda za su gabatar da nasu laccoci dangane da bahasin da aka basu na ilmantar da mahalrta.
Daga cikina bubuwan da za a yi har da gabatar da takaitaccen bayani kan surori 114 da aka gabatar acikin darasi 99 wanda kuma yake a rubuce kuma a nade cikin faifai.
Daga cikin abubuwan da darussan suka kunsa har da tambayoyi ga mai yin nazari, kamar tamabya cewa sau nawa ka karanta kuar’ani? Shin ka fahimci sakon da ke cikin ayoyin da ka karanta? Kuma ko ka amfana da ma’ana ta badini da ke cikin ayoyin?
Wannan na daga cikin abin da wannan zaman bayar da horo zai mayar da hankalia kansa, domin tabbatar da cewa horon ya bayar da ma’anar abin da ake bukata na fahimtar kur’ani da koyarwarsa gad an adam a dukkanin bangarori na zahiri da kuma badini.
2964261