Tun shekaru hudu da suka gatabata ne al’ummar kasar Bahrain suka fara gudanar da gangami da jerin gwano domin neman a gudanar gyaran fuska dangane da yadda ake tafiyar da sha’anin mulki a kasar, inda suka bukaci sarki ya ci gaba da zama kan kujerarsa, amma a baiwa jama’a damar su zabi ‘yan majlaisar dokoki.
Ta yadda majalisar za ta zabi Firayi minista da kanta wanda zai kafa majalisar ministoci, kuma baiwa majalisar dama kafa kwamitin tsara kundin tsarin mulkin kasa wanda zai yi la’akari da hakkokin kowane bangare a kasar, maimakon yadda tsarin kasar yake na mulukiyyah.
Inda sarki shi ne wuka shi ne nama a komai, shi ne ke zabar Firayi minista da ministoci da ‘yan majalisa daidai da ra’ayinsa, ta yadda al’umma ba su da hakki a cikin hakan, bugu da kari kuma dukkanin mukamai a kasar mutane masu alaka da gidan sarautar ne ke rike da su, sauran jama’ar kasar kuma sun zama ‘yan kallo.
Bugu da kari kan hakan kuma al’ummar kasar Bahrain sun bukaci da a rika raba arzikin kasar bisa adalci, maimakon yadda lamarin yake a halin yanzu, baya ga dabaibaye sha’anin mulki da siyasa, hatta ma arzikin kasar na sarki da ‘yayan sarauta da masu alaka da su ne kawai.