Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Financial Times cewa, Nurhan Suwaikan shugabar bababr cibiyar mata musulmi a kasar Jamus ta sanar a jiya cewa kotun kolin kasar Jamus ta janye dokar shekaru da dama da ke hana malamai mata musulmi saka hijabi a makarantu na dukkanin sassan kasar ta Jamus.
Ta ci gaba da cewa wannan babban ci gaba ne aka samu matuka, wanda hakan kuma sakamako ne na gane cewa mabiya addinin muslunci bas u da wata matsala da sauran mutane, su masu son zaman lafiya tare da dukkanin sauran al’iummomi, sabanin kallon da ake yi musu da kuma farfagandar karya a kansu.
A cikin yan kwanakin dai kasar Jamus ta shaeda gangami na mabiya jam’iyyar mai tsananin ki9yya da gaba da addinin muslunci, wadda ke yin kira da jamusawa da sauran al’ummomin turai da su kyamci addinin muslunci, lamarin da a halin yanzu tasirinsa ke raguwa matuka a kasar da ma sauran kasashen turai.
T^a ce sun bayyana farin cikinsu da daukar wanann mataki na baiwa mata musulmi malamai damar gudanar da aikinsu cikin yanci ba tare da wata takura ko hana su yin wani abu na imaninsu ba.
2978668