IQNA

Masarautar Alkhalifa Na Hankoron Mamaye Masallatai Da Husainiyoyin Bahrain

23:35 - March 14, 2015
Lambar Labari: 2984086
Bangaren kasa da kasa, malamain addinin muslunci a kasar Bahrain sun yi kakakusar suka dangane da yunkurin da cibiyar wakafin Ja’afariyya da ke karshen masarautar kasar ken a neman mamaye iko da masallatai da husainiyoyin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Mir’at Bahrain cewa, babbar kungiyar malamai ta kasar ta yi kakakusar suka dangane da yunkurin da cibiyar wakafin Ja’afariyya da ke karshen masarautar kasar ken a neman mamaye iko da masallatai da husainiyoyin kasar baki daya, domin hana mutane gudanar da harkokinsu na addini a cikin yanci.
Bayanin y ace dukkanin masallatai da cibiyoyin addini da ake gudanar da taruka ba mallakin kowa ba ne, suna zaman kansu ne kamar yadda ayake a cikin addini da kuma tsari na kasar, wannan sabon ynkurin na cibiyar wakafin ja’afariyyah da ke karkashin masarautar kasar, wani sabon salo ne na kara danne al’ummar kasar.
Daga karshe malamain sun yi ga mahakuntan kasar da cewa hawainiyarsu ta nisanci tsamiyar dakunan ubangiji da wuraren tarukan addini, matukar dai sun ason zaman lafiya  akasar.
Kamar yadda suka yi kira da a daina yin amfani da wannan suna na mabiya tafarkin iyalan gidan anzo domin cimma manufofi na siyasa da masautar Alkhalifa ke yi a kan al’umma.
2980841

Abubuwan Da Ya Shafa: bahrain
captcha