Kamafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Iram News cewa, Abubakar Bagdadi jagoran ‘yan ta’adda na kungiyar Daesh wato daular muslunci a Iraki da Shamya raya cewa wai ya ga manzon Allah ya ce da shi su fita daga garin Mausil na arewacin kasar Iraki.
Wannan furuci na jagoran ‘yan ta’addan y azo ne sakamakon irin wutar da suke sha a hannun dakarun kasar Iraki a cikin wadannan lokuta, lamarin da ya sanya su fara arcewa daga kasar ta Iraki suna komawa kasashen da suka fito, yayin da wasu kuma suke shga cikin kasar siriya.
Yan ta’addan dai suna samun cikakken goyon baya ne daga wasu kasashen yamamcin turai ne da kuma wasu larabawa, wadanda suke daukar nauyinsu da bas u makudan kudade da kuma makamai masu tarin yawa, da nufin kifar da gwamnatocin da bas u dasawa.
Tun abyan da wannan kungiya tafara gudanar da ayyukanta na ta’addanci, ya zuwa yanzu ta samu jawo hankulan dubban samari daga kasashen larabawa da na turai da kuma yankun asia, wadanda suke hadewa da kungiyar wajen gudanar da mnanan ayyukanta na ta’addanci.
Sakamakon wutar da suke sha hakan ya sanya wasunsu tsrewa sanye da kayan mata daga wasu birane na kasar Iraki, amma an kame wasunsu a lokacin da suke hanoron ficewa, bayan samun bayanai kan shirin nasu, kuma yanzu haka ana tsare da wadanda aka kame a hannun jami’an tsaro.
2985142