Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, a yau ne aka shiga bangare na karshe a gasar karatun kur'ani mai tsarki da kuma harda da ake gudanarwa abababr cibiyar muslunci ta Azhar da ke da babban mazauna a birkin alkahira.
Bayanin ya ci gaba da cewa wanann gasa dai tana samun halaratr dalibai makranta kur'ani mai tsarki daga dukkanin bangarorin kasar Masar kamar dai yadad aka saba gudanarwa a kowace shekara, wanda hakan na daya daga cikin dadaden shirin cibiyar na yada karatun kur'ani da ilmominsa a tsakanin matasa.
Jami'ar dai tana taka gagarumar rawa ta fuskoki da dama domin kara bunkasa wanann gasa da aka saba gudanarwa tsawon shekaru masu tarin yawa, inda aka yi malamai da suka shahara awannan bangare, wanda kuma a halin yanzu jikokinsu ne suke gudanar da shirin wanda ya samu gagarumar nasara adukkanin bangarori.
Kasar Masar dai na daya daga cikin kasashen larabawa da suke bayar da muhimamnci matuk ga harkar karatu da harder kur'ani mai tsarki, wanda hakan ne ma ya sanya kasar ta zama ta daya a duniya a wannan bangare, tafuskkar yawan makaranta da kuma mahardata da suka shahara.
Bayan amamla gasar dai za a bayar da kyutuka ga wadanda suka nuna kwazoa dukaknin bangarorin gasar kamar dai yadda ake yi.