Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yanar gizo na jagora cewa, a sakon day a mika na sabuwar shekarar shamsiyya, jagoran ya bayyana cewa, farkon shekarar bana yayi daidai da ranakun shahadar Nana Fatima (amincin Allah ya tabbata a gare ta). Irin kaunar da mutanenmu suke yi wa Zuriyar Annabi da ‘yarsa mai girma, hakan zai sanya a kula da kuma kiyaye wasu abubuwa, wanda wajibi ne kowa ya kiyaye su; Kuma ko shakka babu za a kiyaye din.
Fatan da muke da shi, shi ne cewa wannan shekarar, ta zamanto shekara mai cike da albarkokin Fatima, sannan kuma sunan wannan mai girmar da kuma ambatonta za su yi gagarumin tasiri cikin rayuwar al'ummarmu a wannan shekara ta 1394. Haka nan kuma muna fatan wannan sabuwar shekarar ta hijira shamsiyya, za ta zamanto shekara mai cike da albarkoki ga al'ummar Iran da dukkanin al'ummomin da suke girmama wannan idi na Nourouz.
Ina isar da gaisuwa da sallama ta ga mai girma Bakiyatullah al-A'azam (rayukanmu su zamanto fansa a gare shi) da kuma jinjinawa Imaminmu mai girma Imam Khumaini da shahidanmu a daidai wannan lokacin, muna rokon Allah Madaukakin Sarki da ya arzurta mu da kuma amfanar da mu da addu'oin wadannan manyan bayin Allah.
Yanzu bari mu yi dubi a yanayi na gaba daya ga shekara ta 1393 (da ta gabata) da kuma wannan sabuwar shekarar wacce ta faro yanzun nan. Shekarar 1393, shekara ce da take cike da abubuwa masu yawa, shin a fagen cikin gida ne ko kuma a fagen kasa da kasa; mun fuskanci kalubale da dama, kamar yadda kuma mun sami ci gaba su ma kala-kala. Bisa la'akari da wadannan kalubalen ne ya sanya tun a ranar farko ta shekarar (da ta gabatan) mu ka ba ta sunan shekarar "Himma Ta Kasa Da Kokari A Fagen Gudanarwa". Idan muka kalli shekarar da ta gabatan kuwa ta 1393, za mu iya ganin bayyanar irin wannan himma ta kasa. Al'ummarmu sun bayyanar da tsayayyiyar azamarsu, shin a fagen jurewa wasu matsalolin da aka kirkiro musu ne, haka nan a ranar 22 Bahman (ranar nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran), haka nan a ranar Kudus da kuma gagarumin jerin gwanon ranar Arba'in (na Imam Husaini) da aka gudanar, lalle sun bayyanar da kuma nuna wannan himma ta su. A fagen gudanarwa ma, alhamdu lillahi lalle an ga irin wannan kokarin a wasu bangarorin. A fagagen da aka yi irin wannan kokarin kuwa, lalle an samu ci gaba masu yawa. Koda yake wannan kira da nasiha ba wai kawai ta takaita da shekarar da ta gabatan ta 1393 ba ce. Lalle al'ummarmu tana bukatar himma ta kasa da kokari a fagen gudanarwa a wannan shekarar, haka nan a dukkanin shekarun masu zuwa.
Amma dangane da shekarar 1394, muna da gagarumin fata ga al'ummarmu masu girma, wadannan dukkaninsu abubuwa ne da za a iya cimma su. Babban fatan da muke da shi ga al'ummarmu a wannan shekarar, shi ne ci gaba na tattalin arziki; karfi da daukaka ta yanki da kuma kasa da kasa; ci gaban ilimi na hakika; adalci wajen shari'a da kuma tattalin arziki; sannan da kuma imani da neman kusaci da Allah wanda shi ne kan gaban dukkanin sauran abubuwan, sannan shi ne ke share fagen isa ga dukkanin wadannan abubuwan da na ambata. A ra'ayina, dukkanin wadannan abubuwan, wasu abubuwa ne da za a iya cimma su. Babu guda daga cikin su da ya fi karfin al'ummar Iran da kuma siyasar wannan tsari na Musulunci. Fagage da kuma karfin da muke da shi, suna da yawan gaske. Akwai abubuwan fadi a wannan bangaren, wanda insha Allahu a cikin jawabin da zan yi da yammacin yau din nan, zan yi ishara da su.
Abin da nake son gaya wa al'ummarmu masu girma a wannan lokacin, shi ne cewa lalle wadannan abubuwa masu girma da muhimmanci za a iya cimma su ne, to amma akwai sharudda. Daya daga cikin wadannan sharuddansa masu muhimmancin kuwa, shi ne aiki tare cikin kauna da fahimtar juna tsakanin jama'a da gwamnati. Idan har aka sami irin wannan aiki taren tsakanin bangarori biyun, ko shakka babu za a iya cimma wadannan abubuwan da muke fatan ganin an cimma su, sannan kuma al'ummarmu masu girma za su ga hakan da idanuwansu. Gwamnati ma'aikaciyar al'umma ce, su kuwa al'umma su ne suka dauke ta aiki. Idan har aka sami fahimtar juna da aiki tare cikin kauna tsakanin jama'a da gwamnati, to kuwa aiki zai ci gaba sosai. Wajibi ne a dogara da juna; gwamnati ta yarda da kuma amincewa da jama'a, ta girmama su da ba su muhimmanci da kuma yarda da irin karfin da suke da shi. Haka nan su ma jama'a su amince da gwamnatin wacce mai musu hidima ce.
Ina da abubuwan fadi da kuma kiraye-kirayen da zan yi a wannan bangaren, wanda insha Allahu, a jawabin da zan yi zan yi ishara da su. A saboda haka a ra'ayina, wajibi ne shekarar bana ta zamanto shekarar aiki tare tsakanin gwamnati da al'umma. Don haka na sanya wa wannan shekarar sunan "Shekarar Jituwa Da Aiki Tare, Tsakanin Gwamnati Da Al'umma". Ina fatan za a tabbatar da wannan taken a aikace, sannan kuma dukkanin bangarori biyun, wato al'ummarmu masu girma, al'ummarmu ma'abociyar himma da jaruntaka, al'umma mai basira da masaniya, da kuma gwamnati ma'abociyar hidima, za su sami damar aiwatar da wannan taken a aikace sannan kuma a ga tasirin hakan a aikace .
Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya taimaki kasarmu wajen samun nasarori cikin dukkanin manyan ayyukan da ta sa a gaba. Kamar yadda kuma na ke rokonsa da ya ba mu damar yin hidima ga wannan al'umma.
3014817