IQNA

Aiki Kowa Daga Cikin Al’umma Shi Ne Bayar Da Gudunmawa Wajen Tafiyar Da Gwamnati

23:21 - March 22, 2015
Lambar Labari: 3026944
Bangaren siyasa, Ayatollah Sayyid Ali Khameenei jagoran juyin juya halin muslunci a Iran,a lokacin da yake gabatar da jawabi a haramin Imam Rida (AS) a gaba dubban daruruwan mutane ya bayyana cewa, bisa la’akari da kalubale da ke gaban gwamnati wajibi ne a kan kowa daga cikin al’umma ya yi abin zai iya domin bayar da tasa gudunmawa.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin yanar gizo na jagora cewa, a  yammacin ranar Asabar da ta yi daidai da ranar farko na sabuwar shekarar 1394 hijira shamsiyya, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gabatar da jawabinsa na sabuwar shekara a haramin Imam Ali bn Musa al-Ridha (a.s) da ke birnin Mashad inda yayi karin haske kan batutuwa daban-daban da suka shafi kasar Iran da kuma taken da aka ba wa shekarar ta bana wato "Shekarar Jituwa Da Aiki Tare, Tsakanin Gwamnati da Al'umma". A jawabin nasa Jagoran yayi karin haske kan nauyin da ke kan wadannan bangarori biyu, wato goyon bayan al'umma ga gwamnati da kuma wajibcin hakurin jami'an gwamnati dangane da sukan da ake musu wadanda suka yi daidai da hankali. Har ila yau kuma Jagoran yayi ishara da wasu tushe guda hudu da gwamnatin Musulunci ta ginu a kansu, bugu da kari kan dama da kuma kalubalen da suke gaban gwamnatin inda ya ce: Tsara manufofi da kuma tsare-tsaren kai wa gare su bugu da kari kan ci gaban kasa da karfafa tattalin arziki sannan da kuma taimako da goyon bayan al'umma musamman musamman ‘yan kasuwa da kafafen watsa labarai wajen ciyar da tattalin arzikin kasa, a matsayin babban nauyin da ke kan kowa.
Haka nan kuma yayin da yake magana dangane da tattaunawar da take gudana kan shirin nukiliyan Iran kuwa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: A Iran babu wani mutum da ke adawa da magance matsalar nukiliyan ta hanyar diplomasiyya, to sai a bangare guda kuma al'ummar Iran, jami'an gwamnati da tawagar da take tattaunawar ba za su taba yin kasa a gwiwa a gaban girman kai da takama da karfin Amurka ba. Sannan kuma ta hanyar tsayin daka, za su yi nasara cikin wannan babbar jarabawar da take gabansu.
Har ila yau yayin da yake ishara da wata aya ta Alkur'ani mai girma, Ayatullah Khamenei ya bayyana wasu abubuwa guda hudu, wato ‘salla, zakka, umurni da kyakkyawa da hani da mummuna' a matsayin wasu tushe kuma kashin baya na tsarin gwamnatin Musulunci inda ya ce: Allah Madaukakin Sarki yayi alkawarin cewa duk wata al'umma da take da ta kiyaye wadannan siffofi guda hudu, to kuwa zai taimaka mata, kuma za ta fice daga ikon masu takama da karfi kuma ja'irai.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Kowane guda daga cikin wadannan abubuwa guda hudu, yana da bangare na daidaiku da kuma na al'umma wajen aiwatar da shi, don haka ne yake da tasirin gaske cikin tsarin gwamnatin Musulunci.
Yayin da yake karin haske kan bangare na daidaiku da ke cikin salla da kuma tasirin hakan wajen samar da sa'ada da ci gaban mutum mumini, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: A daidai wannan lokacin, salla tana da bangarori na al'umma da zamantakewa da kuma share fagen hado zukatan musulmi waje guda zuwa ga wata cibiya guda.
Haka nan kuma yayin da yake magana kan rawar da zakka take takawa wajen karfafa ruhin rufe ido da yafuwa cikin rayuwar dan'adam, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: A fagen zamantakewa, zakka tana nuni da cewa wani mutum musulmi ba zai iya zama dan ba ruwanmu dangane da halin da al'ummarsa na daga raunana da talakawa da mabukatan cikinta ba.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana ‘umurni da kyakkyawa da hani da mummuna' a matsayin tushe da kashin bayan dukkanin hukunce-hukuncen Musulunci. Haka nan kuma yayin da yake bayanin cewa wajibi ne a kan dukkanin muminai a duk inda suke a duniyar nan da su taimaka wajen kwadaitar da kyawawan ayyuka da kuma jan kunne dangane da fadawa tarkon munanan ayyuka, Jagoran cewa yayi: Abin da ya zama wajibi a lura da shi da kuma ba shi muhimmanci, shi ne babban umurni da kyawawan halaye, wato samar da tsarin Musulunci da kuma kiyaye shi.
Jagoran ya bayyana kiyaye mutumcin al'ummar Iran, kyautata al'adu, gyara yanayi da kyawawan halaye, samar da yanayi na iyali mai kyau, yawaitawa da kuma tarbiyyantar da matasa da suke shirye wajen daukaka kasarsu, karfafa fagen samar da kayayyakin bukata da kuma tattalin arziki na kasa, karfafa kyawawan halayen Musulunci a cikin al'umma, fadada ilimi da fasaha, tabbatar da adalci na shari'a da kuma tattalin arziki, kokari wajen tabbatar da hadin kai na Musulunci, daukaka da kuma karfafa al'ummar musulmi a matsayin wasu manyan kyawawan ayyuka wanda ya zama wajibi a kan kowa yayi kokari wajen ganin an cimma su.
Haka nan kuma yayin da yake magana kan munkari da munanan ayyuka kuwa, Jagoran yayi ishara da lalata al'adun mutane, taimakon makiya, raunana tsari da kuma al'adun Musulunci da raunana tattalin arziki, ilimi da fasaha a matsayi manyan alamu na ayyukan munkarin, daga nan sai ya ce: Allah Madaukakin Sarki a matakin farko, sannan sai Annabi (s.a.w.a) da Imamai (a.s) suna daga cikin manyan masu umurni da kyawawan halaye da kuma hani da munana. Don haka wajibi ne a kan dukkanin muminai a duk inda suke a duniya su yi aiki da wannan farali na Ubangiji.
A ci gaba da jawabin nasa, Ayatullah Khamenei yayi karin haske kan taken da aka ba wa wannan shekara ta bana ta hijira shamsiyya, wato "Shekarar Jituwa da Aiki Tare, Tsakanin Gwamnati da Al'umma" inda ya ce zaban wannan taken da aka yi ma ya ginu ne bisa wadannan tushe guda hudu don tabbatar da jituwa da aiki tare tsakanin mutane da tsarin Musulunci. Jagoran ya ci gaba da cewa: Musulunci yana fatan ganin an samu hadin kai, aiki tare da kuma taimakawa juna tsakanin dukkanin bangarori na al'umma. A saboda haka wajibi ne dukkanin mutane su zamanto masu goyon baya da taimakon kowace gwamnatin da take karkashin tsarin Musulunci, hatta wadanda ba su kada mata kuri'a ba.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana magana guda da aiki tare tsakanin mutane da gwamnati musamman a wajajen da kasa ta ke fuskantar kalubale masu muhimmanci a matsayin wani lamari da ya zama wajibi inda ya ce: A yau nauyin da ke wuyan dukkanin al'umma shi ne su taimaka wa jami'an gwamnati da kuma goyon bayansu.

Jagoran ya bayyana taimako da goyon bayan gwamnatoci a matsayin wani tabbataccen abu wanda kuma na koyaushe. Haka nan kuma yayin da yake jaddada wajibcin ci gaba da yin hakan, Jagoran cewa yayi: Babban abin da dukkanin gwamnatocin suka sa a gaba shi ne magance matsalolin da al'ummar Iran suke fuskanta gwargwadon iyawarsu. A saboda haka wajibi ne kowa da kowa ya taimaka wa gwamnatocin wajen magance matsalolin da mutane suke fuskanta.

Ayatullah Khamenei ya bayyana samun kuri'ar mafiya yawan al'umma a matsayin abin da ke shafe fagen halalcin gwamnatoci a hukumance, don haka sai ya ce: Abu mai muhimmanci ba shi ne kashi nawa cikin dari na kuri'un da aka kada wa wani shugaban kasa ba ne, face abin da ke da muhimmanci shi ne cewa duk gwamnatin da mafi yawan al'umma suka zaba, to a bisa doka tana da halalci. Don haka wajibi ne mutane gwargwadon iyawansu su taimaka mata.

A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayi karin haske dangane da batun sukan ayyukan da gwamnatin ta yi da ba su dace ba inda yayi bayanin yadda ake sukan da kuma irin yadda ya kamata a ce gwamnatin tana mu'amala da masu sukan nata.

Yayin da ya ke bayyana cewar samun masu sukan ayyukan kowace gwamnati a matsayin wani lamari da aka saba da shi, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa ya yi: Wannan gwamnatin ma, tamkar sauran gwamnatocin da suka gabata, tana da masu suka. Babu wata matsala cikin hakan a samu wasu mutane wadanda ba su amince da ayyuka da siyasar gwamnatin ba don haka su yi suka. To amma wajibi ne sukan ta kasance daidai da hankali.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Ni kai na na kasance ina sukan ayyukan gwamnatoci daban-daban, sannan kuma a duk wani wajen da na yi imanin akwai bukatar a yi suka, lalle na kan yi bayani da kuma suka da kuma tunatar da su. To sai dai ina yin hakan ne ta hanyoyin da suka dace.

Daga nan sai Jagoran yayi bayani da karin haske kan sukar da ta dace da hankali inda ya ce: Bai kamata sukan ta zamanto ta yadda za a kawar da irin yardar da mutane suke da ita ga jami'an da suke gudanar da ayyukansu ba, ta yadda za su yanke kauna da gwamnatin. Haka nan kuma bai kamata sukar ta zamanto tare da cin mutumci da kokarin zubar da mutumci ba.

Jagoran ya bayyana mu'amalar da take cike da ‘yan'uwantaka ta Musulunci tare da kaunar juna da tausayawa a matsayin wani abin lura yayin da ake sukan. Daga nan sai ya ce: Tabbas wannan nasiha ce ga dukkanin bangarori biyu. Wajibi ne dukkanin jami'an gwamnati a dukkanin bangarori uku na gwamnatin su kiyaye wannan kan iyakan. Su yi mu'amalar da ta dace da masu sukansu ba tare da cin mutumci da wulakantarwa ba. Don kuwa cin mutumci da wulakanta masu sukan jami'an, lamari ne da ya saba wa hikima.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Ni dai ba ina kiran al'ummarmu masu girma da su nuna halin ko in kula da kuma kawar da kai daga ayyukan gwamnati ba ne. Face ma dai ina kiransu ne da su zamanto masu nuna damuwa da lamurran kasa. Abin da kawai na ke cewa shi ne bai kamata mu'amalar mutane da kuma gwamnati ta zamanto da nufin zubar da mutumcin wani ba.

Jagoran ya ci gaba da cewa: A samu wasu mutane suna nuna damuwarsu kan wani lamari da ya shafi kasar nan, lalle hakan ba laifi ba ne sannan kuma babu wani abin da ya hana hakan. To sai dai bai kamata hakan ya zamanto wata hanyar na tuhuma da rufa ido kan kokari da hidimar da ake yi ba. A bangare guda ita ma gwamnati da magoya bayanta, bai kamata su ci mutumcin mutanen da suke bayyanar da damuwa da kishinsu ba.
Haka nan kuma yayin da yake magana kan irin dabi'arsa ta goyon bayan dukkanin gwamnatocin Iran da suka gabata, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: Ita ma wannan gwamnatin zan ci gaba da goyon bayanta. Koda yake ni dai ba zan goyi bayan kowa ido rufe ba, face dai zan yi hukunci ne bisa ayyukan mutane.
A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da irin gagarumar dama da kuma kalubalen da ake fuskanta, daga nan sai ya ce: Da yardar Allah ana iya yin nasara kan wadannan kalubalen ta hanyar tsare-tsare masu kyau da kuma amfani da dama da irin karfin da ake da shi.
Ayatullah Khamenei ya bayyana karfi na jama'a masu fasaha da kirkiro sabbin abubuwa wadanda mafiya yawansu matasa ne da kuma aiki tare tsakanin jama'a da gwamnatin Musulunci a matsayin wasu daga cikin irin wadannan dama masu girma da ake da su a kasar Iran, daga nan sai ya ce: Duk da irin gagarumar farfagandar da kafafen watsa labaran makiya suke yi a kan matasan Iran, don su sanya su yanke kauna ga makomarsu ko kuma su yi fito na fito da gwamnati ko kuma su kautar da su daga tafarkin gaskiya, to amma ana iya ganin yadda miliyoyin matasa suka fito kan tituna a duk fadin kasar nan yayin jerin gwanon ranar 22 ga watan Bahman da kuma bayyanar da tsananin kaunarsu ga wannan tsari na Musulunci da kuma marigayi Imam Khumaini (r.a).
Jagoran ya bayyana ci gaban ilimi da aka samu a kasar Iran a daidai lokacin da kasar take cikin takunkumi tattalin arziki a matsayin wata babbar dama ta daban din da ake da ita a kasar Iran, daga nan sai ya ce: Ayyukan ci gaba da nasarorin da aka samu a shekarun baya-bayan nan ciki kuwa har da kaddamar da gagarumar tashar man fetur da ke kudancin Iran, makamai na zamani masu ban mamaki ga makiya da aka nuna a yayin atisayen da dakarun soji suke yi, dukkanin su an cimma su ne a lokacin da makiya suke fadin cewa sun sanya wa Iran takunkumi mai ruguzarwa.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana takunkumin da aka sanya wa Iran din a matsayin wata dama duk kuwa da cutarwar da ke cikin hakan. Haka nan kuma yayin da yake magana kan wasu kalubalen da suke gaban gwamnatin kasar Iran, Jagoran cewa yayi: Daya daga cikin manyan kalubalen da suke tinkarar kasar nan, shi ne batun tattalin arziki na kasa da kuma magance matsalar tattalin arziki da rayuwa ta mutane. Wanda hakan wani lamari ne da ke bukatar wannan gagarumin hobbasa da kuma aiki tukuru.
Haka nan kuma yayin da yake magana kan shawarwarin da ya bayar a shekarun baya dangane da irin yadda makiya suka ba da dukkanin himma da karfinsu wajen cutar da tattalin arzikin Iran da kuma bukatar kokari tukuru daga bangaren jami'an gwamnati, Ayatullah Khamenei cewa yayi: Masu bakar aniya kan al'ummar Iran a fili suke fadin cewa manufarsu ta yin wannan matsin lamba na tattalin arziki, wata manufa ce ta siyasa, wato haifar da rashin yarda da fushi cikin zukatan mutane da kuma dagula lamurran tsaron kasar nan ta hanyar tunzura mutane su yi bore wa gwamnati.
Jagoran ya bayyana cewar fada da wannan kalubalen yana bukatar hadin gwiwa da aiki tare tsakanin bangarori daban-daban na gwamnati da kuma kara himma da muhimmanci ta bangaren jami'an gwamnati. A wannan bangaren ma dai Jagoran yayi ishara da kuma janyo hankali kan wasu batutuwa guda hudu.
Jaddadawa kan wajibcin yunkuri wajen fada da siyasar gaba da kiyayya ta Amurka a fagen tattalin arziki, shi ne batu na farko da Ayatullah Khamenei yayi bayani kansa inda yayi ishara da mahanga guda biyu da ake da su a kasar Iran kan yadda za a magance matsalar tattalin arzikin da ake fuskanta a kasa.
Jagoran ya ce: Wata mahangar ta yi amanna ta yi amanna da cewa wajibi ne a yi amfani da irin karfi da damar da ake da su a cikin gida wajen karfafa tattalin arzikin, wadanda ya zuwa yanzu ba a ba su muhimmancin da ya dace da su ba, ko kuma ma ba a yi amfani da su din ba.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Mahanga ta biyu ita ce kishiyar ta farko, masu mahangar sun yi amanna da cewa za a iya samun ci gaban tattalin arziki ne ta hanyar dogaro da kasashen waje. A saboda haka wajibi ne mu sauya siyasarmu ta waje, mu tafi tare da ma'abota girman kai da masu tinkaho da karfi. Mu mika musu wuya don mu magance matsalolin tattalin arzikin da muke da su.
Ayatullah Khamenei ya jaddada cewar: Tabbas wannan mahanga ta biyu, kuskure ne. Hakan ba za ta taba haifar da da mai ido ba. Babu wata fa'ida cikin hakan.
Yayin da yake ishara da kuskuren wannan mahangar, Ayatullah Khamenein cewa yayi: Takunkumin da kasashen yammaci suka sanya wa al'ummar Iran a halin yanzu babban dalili ne dake tabbatar da kuskuren wannan mahanga ta dogaro da waje wajen karfafa tattalin arziki. Don kuwa babu wani haddi da masu tinkaho da karfi za su ji cewa sun wadatu. Sannan kuma wasu abubuwan haka nan kwatsam ake shigo da su kamar shirin da aka tsara na rage farashin man fetur a kasuwar duniya wanda ya haifar da ‘yan matsaloli ga tattalin arzikin kasar nan.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: A yau dukkanin kokarin masu kiyayya da al'ummar Iran shi ne karfafa wannan mahanga ta biyu. A saboda haka ne ma shugaban kasar Amurka cikin sakonsa na Nourouz ya ke gaya wa al'ummar Iran cewa matukar ba ku amince da bukatunmu a tattaunawar nukiliya da ake yi ba, to kuwa ba za a taba samun ci gaban tattalin arziki a kasar Iran ba.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Dogaro da kasashen waje wajen karfafa tattalin arziki, ba zai taba haifar da da mai ido ba. Don haka wajibi ne a koda yaushe mu fi ba da muhimmanci ga amfani da irin karfi da damar da muke da su a cikin gida. Wannan kuwa shi ne abin da tattalin arziki na dogaro da kai da muka gabatar yake magana kai, wato karfi na cikin gida da kasar Iran da kuma al'ummar Iran suke da shi.
Batu na uku da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya tunatar kansa a bangaren tattalin arzikin, shi ne wajibcin ayyana manufa da siyasar da ake son cimma bugu da kari kan nesantar ba da muhimmanci ga abubuwan bayan fage.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Babbar manufar da ya wajaba jami'an gwamnati da al'ummar kasa su ba da himma wajen cimma ta, shi ne ba da muhimmanci ga batun samar da kayyakin bukata a cikin gida.
Yayin da yake magana kan hanyoyin da za a bi wajen karfafa kayayyakin da ake samarwa a cikin gida, Jagoran cewa yayi: taimako da goyon bayan kananan kamfanoni, samar da wani yunkuri na rage dogaro da man fetur, saukaka hanyoyin zuba jarri, rage irin kayayyakin da ake shigowa da su daga waje da kuma fada da fasa kwabrin kayayyaki, wadanda wasu hanyoyi ne na goyon bayan kayayyakin da ake samarwa a cikin gida. Tabbas bankuna za su iya taka rawa mai kyau ko kuma mara kyau a wannan bangaren. A saboda haka wajibi ne jami'an bankunan kasar nan su ba wa wannan lamarin muhimmanci na musamman.
Yayin da ya koma kan batun na hudu kuma na karshe kan batun tattalin arziki na kasar, Jagoran cewa yayi: Takunkumin shi ne kawai makamin makiya wajen fada da al'ummar Iran. A saboda haka idan har muka yi tsari mai kyau da kuma dogaro da irin karfi na cikin gida da muke da shi, aka yi ayyuka masu kyau, to kuwa za a samu damar rage irin tasirin da takunkumin yake da shi, sannan kuma za a iya kai wa ga gaci.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: Matukar dai jami'an gwamnati da sauran al'ummar gari da ‘yan kasuwa suka ba da himma, sannan kuma kafafen watsa labarai su ma suka shigo ciki, to kuwa za ku ga yadda wadannan takunkumin za su gaza wajen hana al'ummar Iran ci gaban da suka faro.
A ci gaba da jawabin nasa, Ayatullah Khamenei yayi magana da karin haske kan batun tattaunawar da Iran take yi da manyan kasashen duniya inda yayi karin haske kan wasu batutuwa.
Yayin da yake magana kan tsare-tsaren da siyasar masu tattaunawa da Iran din wadanda a mafi yawan lokuta Amurkace, Ayatullah Khamenei cewa yayi: Lalle Amurkawa suna tsananin bukatar wannan tattaunawar, sabanin da ake samu a tsakaninsu ma kan wannan batu ne. Don haka ne ‘yan hamayyar wannan gwamnatin ta Amurka suke takokari wajen ganin sun rubuta wannan nasarar da aka samu ga gare su da kuma jam'iyyarsu
Haka nan kuma yayin da yake ishara da sakon Nourouz da shugaban Amurka ya aike wa al'ummar Iran, da kuma rashin gaskiyar da ke cikin abubuwan da ya fadi, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: A cikin sakon nasa, shugaban kasar Amurkan yana cewa akwai wasu mutane a Iran da suke adawa da magance matsalar nukiliyan ta hanyar diplomasiyya. Lalle hakan karya ce. Don kuwa babu wani mutum a Iran da ke adawa da magance wannan matsalar ta hanyar diplomasiyya da tattaunawa.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Abin da al'ummar Iran suke adawa da shi, shi ne tinkaho da karfi da tursasawar da gwamnatin Amurka take yi, wanda al'ummar Iran sun tsaya kyam wajen tinkarar hakan.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Babu guda daga cikin jami'an gwamnati ko ‘yan tawagar tattaunawar ta Iran ko kuma al'ummar kasar da zai amince da girman kan Amurka.

Har ila yau kuma yayin da yake jaddada cewa tattaunawar da Iran take yi da Amurka kan batun nukiliya ne kawai ban da sauran abubuwa, Jagoran cewa yayi: Ba za mu taba tattaunawa da Amurka kan batutuwan mu na cikin gida da na yanki da kuma batun makamai ba. Don kuwa siyasar Amurka a yankin nan ita ce haifar da rashin tsaro a yankin nan da fada da al'ummomin yankin nan da kuma farkawa ta Musulunci da ake samu, wanda hakan kishiyar manyan siyasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne.
Haka nan kuma yayin da yake magana kan maganganun da Amurkawan suke yi na cewa za a dage wa Iran takunkumi ne bayan an cimma yarjejeniya da kuma dubi cikin ayyukanta (kan abubuwan da aka cimma din), Jagoran ya bayyana hakan a matsayin wata yaudara da al'ummar Iran ba za su taba amincewa da shi ba inda ya ce: Lalle wannan magana ce da za a amince da ita ba. Don kuwa dage takunkumin wani bangare ne na tattaunawar da ake yi, ba wai sakamakon tattaunawar ba. A saboda haka kamar yadda mai girma shugaban kasa a fili ya fadi, wajibi ne dage takunkumin ya biyo bayan cimma yarjejeniyar ba tare da bata lokaci ba.
Har ila yau yayin da yake magana kan maganganun Amurkawan na cewa wajibi ne ya zamanto cewa Iran ba zata iya yin watsi da duk wata yarjejeniyar da aka cimma da ita ba, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: wannan ma dai ba abin amincewa da shi ba ne, don kuwa idan har su ma sun amincewa wa kansu na su yi watsi da abin da aka cimma din saboda wasu dalilinsu da kuma dawo da takunkumin. Don haka babu dalilin da zai sanya mu ma mu amince da wata matsayar da ba za mu iya sauya ra'ayi kanta ba.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da ikirarin Amurkawa na cewa har ya zuwa yanzu Iran tana kokarin mallakar makaman kare dangi, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: Su kansu sun san cewa hatta a wannan tattaunawar ta nukiliya Iran tana girmama duk wata yarjejeniya ta kasa da kasa da kuma siyasarta ta cikin gida. Ba mu taba karya alkawari ba. A daya bangaren kuwa Amurkawa sun sha karya alkawarinsu.
Ayatullah Khamenei dai ya ci halayen Amurkawa a yayin wannan tattaunawar ta nukiliya abin daukan darasi ne a cikinsa inda ya ce: Lalle halayen Amurkawa abin daukar darasi ga masana da ‘yan boko na cikin kasar nan don su gano da wa mu ke tattaunawar, sannan kuma yaya Amurka take mu'amala da sauran mutane.
Har ila yau kuma yayin da yake ishara da wasu barazana da Amurka take yi kan yiyuwar amfani da karfin soji ko kuma kara karfafa takunkumin da suka sanya wa kasar Iran matukar dai aka gagara cimma yarjejeniyar, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa yayi: Wadannan barazanar dai ba sa tsorata al'ummar Iran. Don kuwa wannan al'ummar a tsaye take, sannan kuma cikin dukkanin daukaka da nasara za ta fito daga wannan babbar jarrabawar.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce taimako na Ubangiji shi ne babban abin da ya tabbatar wa al'ummar Iran da nasararorin da take samu a fagage daban-daban.
3019887

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha