Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Akhbar Al-yaum cewa, bisa ga dokar kasar Turkiya an hana mata sojoji da kuma matan jami'an tsaro saka hijabi a barikokinsu, amma yanzu babbar kotun koli a kasar ta Turkiya ta janye dokar hana sanya hijabi mata sojoji ko kuma matan jami'an tsaro a kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan hukunci ya samu karbuwa daga sojoji mata da suke gudanar da ayyukansu a barikoki, kamar yadda su kansu matan sojoji da ke barikokin da mazajensu, sun nuna gamsuwa da wannan mataki da kotun kolin kasar ta dauka.
Kasar Turkiya dai na daga cikin kasashen musulmi da suke fama da matsaloli na takura ma musulmi dangan eda bin koyarwar addininsu, duk kywa da cewa mahukuntan kasar a halin yanzu sun rage irin wannan matsin lambar idan aka kwatanta da lokutan baya.
3040119