
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bawwabah News cewa makaranta 452 ne suke halartar wannan gasa da aka fara gudanarwa, kuma 14 daga cikin makarantan mata ne.
Bayanin ya ci gaba da cewa an fara gudanar da gasar ne bayan tantance makaranta suka zo a mataki na farko da na biyu da na uku a irinta da aka gudanara sauran yankunan kasar, inda aka zabo wadanda suka nuna kwazo domin halartar bababr gadar a fadar mulkin kasar.
Gasar ta bana dai ba ta takaitu da bangaren tajwidi ba kawai, har ma ta hada wasu bangarorin ilmomin addinin muslunci, kamar yadda kuma ba a bana an samu wadanda shekarunsu sun kai 40 da suke halartar gasar, sabanin shekarun baya.
Za a bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka nuna kwazoa dukaknin bangarorin da ake gudanar da gasar a kansu, wanda kuma ake sa ran kamala ta acikin mako mai zuwa idan mai kowa ya kai mu.