IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Karatun Kur’ani Mai Taken Tajul Kur’an A kasar Aljeriya

18:44 - April 05, 2015
Lambar Labari: 3092634
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wata gasar karatun kur’ani mai tsarki mai taken tajul kur’an 2015 a kasar Algeriya tare da halartar makaranta daga sassa na kasar a babbar cibiyar Wlud Abdulrahman Kaki a garin Mustaganam.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na reflexiondz cewa, wannan gasa da aka fara gudanarwa da gidan radioyon kur’ani na kasar ke watasawa, ma’aikatar kula da harkokin al’adu ta kasar ce ta dauki nauyin shiryata da kuma gabatar da ita.
Bayanin ya ci gaba da cewa gasar ta Tajul kur’an 2015 tana samun halartar masu gasa 34 da suka hada da maza 20 da kuma mata 14 da suke da shekaru 28 har zuwa 40 daga sassa daban-daban na kasar.
Ana sa ran kamala wannan gasa a cikin kwanaki uku masu zuwa, inda za a bayar da kyautuka na bai daya, da kuma wasu kyautukan na muswamman ga wadada suka nuna kwazo a dukkanin bangarori na harda da kuma karatu.
Kasar dai na daga cikin kasashen da suke bayar da muhimamnci matuka ta fuskar karfafa matasa wajen shiga gasar karatun kur’ani mai tsarki a mataki na cikin kasa da kasa, da kuma irinta ake gudanarwa a duniya.
3089328

Abubuwan Da Ya Shafa: algeria
captcha