Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Rasad cewa, Muhamamd Mukhtar Juma’a ministan kula da harkokin addinin musunci a kasar Masar ya bayar da lambar kyautar sulhu da zaman lafiya ga Ayatollah Sayyid Muhamamd Baqer Al-Mehri babban malamin shi’a kuma wakilan manyan malaman mabiya wannan mazhaba a kasar Kuwait tare da mabiyansa.
Wannan mataki da ministan na kasar Masar ya dauka ya fuskanci akkausar daga wasu daga cikin masu tsatsauran ra’ayin bangaranci na mazhaba, inda suke kallon hakan a matsayin wani lamari da bai dace ba a mahangarsu, domin yin hakan tamkar amincewa ne da shi’a a hukumance da kuma karfafa ta.
Kasar Masar dai ta bi sahun sauran kasashe ‘yan amshin shatan Amurka wajen kaddamar da hare-hare kan al’ummar kasar Yemen, inda suke ci gaba da kasha mutane babu ji babu gani mata da kananan yara.