IQNA

Masu Kiyayya Da Musulunci Sun Gudanar Da Zanga-Zanga A Birnin London

22:41 - April 06, 2015
Lambar Labari: 3100055
Bangaren kasa da kasa, masu tsananin kiyayay da addinin muslunci a kasar Birtaniya sun gudanar da gangami a karon farko a birnin London na kasar Biratniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na On Islam cewa, daruruwan masu tsananin kiyayay da addinin muslunci a kasar Birtaniya sun gudanar da gangami a karon farko a birnin London ammakuma sun hadu da masu kiyayya da nuna banbanci da bangarenci.
Wannan na daga cikin irin hankoron da kungiyar ta PEGIDA ke yia  cikin kasashen turai da nufin yada mummunar akidarta ta nuna kiyayya ga mabiya addinin muslunci mazauna nahiyar turai da ma sauran musulmi na duniya baki daya, lamarin da ke fuskantar turjiya daga masu kiyaya da wanann akida.
‘Yan kungiyar ta PEGIDA sun fara harkokinsu ne daga kasar Jamus, kafin daga bisani wanann mummunar akida ta bazu zuwa wasu daga cikin kasashen yammacin nahiyar turai, da hakan ya hada har da ita kanta kasar Birtaniya inda kimanin magoya bayansu 2000 suka yi gangami, lamarin da ake kallonsa a matsayin bababn ahadari ga wadanann kasashe.
Bullar wadannan kungiyoy a cikin kasashen turai, ya sanya wasu daga cikin gwamnatocin yin tunanin daukar matakan da suka dace domin fuskantar lamarin yadda ya kamata, domin shawo kansa.
3095703

Abubuwan Da Ya Shafa: london
captcha