IQNA

Musulmin Hong Kong Na Kokarin Wayar Da Kan Mutane Dangane Da Musulunci

23:49 - April 08, 2015
Lambar Labari: 3110942
Bangaren kasa da kasa, jagororin mabiya addinin muslunci a yankin Hong Kong na iyakacin kokarinsu domin wayar da mutane kan yadda suke kallon addinin muslunci a yankin domin ba su masaniya ta hakika akan wannan addini.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na China Morning Post cewa, musulmin kokarinsu domin wayar da mutane kan yadda suke kallon addinin muslunci a yankin domin ba su masaniya kan muslunci.
A cikin bayanin an bayayna cewa kimanin kungiyoyin 21 ne suka goyi bayan bayanin a ikin harsunan turanci da Cananci na musulmi dangane dangane da abin suke fada kan addininsu cewa ba addinin ta’addanci ba ne kuma suna son zaman lafiya da kowa.
An bayyana abubuwan da suke faruwa yanzu a wasu na ayyukan ta’addanci a matsayin abbabna bin da ke tasirin wajen jawowa musulmi tsana a yankin, musamman ma mata daga cikinsu.
Adel Malek daya ne daga cikin malamai da suke koyar addinin muslunci kuma yake koyar da harshen turanci ya bayyana cewa, akwai nuna banbanci da ake yia  cikin kowace jama’a, amma dai yankin Hong Kong na daga cikin wurare da wanann lamari bai tasiri sosai ba.
Ya kara da cewa babbar manufarsu ta fitar da wannan bayani na sulhu kara wayar wa al’ummar yankin da kai kan muhimamncin sanin addinin muslunci ta hanyoyin da suka kamata, maimakon dogaro da abin da suke ji ana fada kan muslunci.
3102066

Abubuwan Da Ya Shafa: Hong Kong
captcha