Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin jagora cewa, a lokacin da jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da wasu gungun mata, mawaka da masu yabon Ahlulbaiti (a.s) don tunawa da zagayowar ranar haihuwar ‘yar Manzon Allah, Fatima al-Zahra (a.s) ya taya al'umma murnar wannan rana mai albarka sannan kuma yayi karin haske kan batutuwa masu muhimmancin gaske dangane da batun tattaunawar nukiliya da Iran take yi da manyan kasashen duniya da kuma abin da ke faruwa a kasar Yemen. Jagoran y ace wasu suna tambaya cewa me yasa bai bayyana matsayinsa dangane da tattaunawar da ake yi da manyan kasashen duniya ba?
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: Dalilin da ya sanya Jagora bai fadi ra'ayinsa ba shi ne babu wani abin fadin ra'ayin da ya faru don kuwa jami'an gwamnati da jami'ai masu kula da lamarin nukiliyan suna cewa har yanzu babu abin da aka yi, kuma babu wani batu dake wajabta wani abu tsakanin bangarori biyun da aka yi.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: A irin wannan yanayin babu bukatar daukar matsaya.
Jagoran ya ce: Idan da za a tambaye ni cewa: "Shin ka amince da tattaunar nukiliya na baya-bayan nan ko kuma a'a", to abin da zan ce shi ne ni dai ban amince ba sannan kuma ba na adawa da hakan, don kuwa har ya zuwa yanzu babu wani abin da ya faru.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Dukkanin matsalar za ta kunno kai a lokacin da aka zo bahasi da tattaunawa kan rassan lamurran. Saboda kuwa bangaren da ake tattaunawa da shi din (Amurka) mai karya alkawari ne, mai mummunar mu'amala sannan kuma ha'ini ne. Mai yiyuwa ne a lokacin da ake tattaunawa rassa da kananan abubuwan ya ha'inci kasa da al'ummar da yake tattaunawa da ita.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Abin da a halin yanzu ya faru, ba shi asalin yarjejeniyar ba sannan kuma ba shi ne zai lamunce cewa za a cimma yarjejeniyar ba, kai ba ma abu ne da zai lamunce cewa za a kai ga gaci a tattaunawar ba. A saboda haka ba wani lamari ne na taya murna ba.
A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da kuma taunatarwa kan wasu batutuwa inda ya ce: Ni dai babu wani lokaci da na taba zama ina da wani kyakkyawan fata dangane da tattaunawa da Amurka. Hakan kuwa ba wai bisa zato ba ne face dai saboda abubuwan da suka faru ne a baya.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Idan a nan gaba aka fitar da dukkanin abubuwan da aka tattauna da kuma rubutawa a yayin tattaunawar, a nan ne kowa zai fahimci inda aka sa gaba sannan kuma da me muka dogara da wannan magana ta mu.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Duk da cewa ba ni da kyakkyawan fata da tattaunawa da Amurka, to amma duk da haka na goyi bayan wannan tattaunawar. A halin yanzu ma ina ci gaba da goyon bayan hakan.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: Ni dai dari bisa dari ina goyon bayan duk wata yarjejeniyar da za a cimma wacce za ta lamunce daukakar al'ummar Iran. Idan har wani ya ce Jagora yana adawa da cimma yarjejeniyar, lalle hakan ba gaskiya ba ce.
A ci gaba da bayanin da yake yi kan amincewarsa da duk wata yarjejeniyar da za a cimma wacce za ta lamunce daukakar al'ummar Iran, Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Koda yake ya kamata a san cewa "rashin cimma yarjejeniya shi ya fi kyau a kan mummunar yarjejeniya" don kuwa akwai daukaka cikin rashin yarda da yarjejeniyar da take son take hakkoki da daukakar al'ummar Iran a kan amincewa da yarjejeniyar da take son kaskantar da al'ummar Iran.
Daga nan sai Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi karin haske kan wani lamari mai muhimmanci da ake fadi inda ya ce: A wasu lokuta wasu suna fadin cewa dukkanin rassa da kananan abubuwan da ake tattaunawar karkashin kulawar Jagora ne, lalle ba haka lamarin yake ba.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Lalle ban kasance dan ba ruwanmu dangane da tattaunawar da ake yi ba, to amma ba na tsoma baki cikin kananan abubuwan da ake tattaunawa, a nan gaba ma ba zan tsoma baki ba.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Ni dai dangane da manyan batutuwa, asalin tafarkin da ya kamata a bi da kuma iyakokin da bai kamata a tsallake su ba ne a mafi yawan lokuta na kan sanar da shugaban kasa, a wasu lokutan kuma ga ministan harkokin waje. To amma kananan abubuwa da rassansu yana hannunsu ne.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: Ni dai na yarda da jami'ai masu tattaunawar. Sannan kuma ya zuwa yanzu ba ni da shakku kansu, insha Allahu a nan gaba ma haka lamarin zai kasance. To amma ina da wasu damuwa masu girma kan lamarin.
Yayin da yake magana kan bangaren da ake tattaunawa da shi din wanda ma'abocin yaudara da karya da karya alkawari ne da kuma dalilin irin damuwa da rashin tabbas din da yake da shi kan wannan lamarin, Ayatullah Khamenei cewa yayi: Ana iya ganin misalin irin wannan dabi'ar ta su cikin tattaunawar karshen da aka yi. Kimanin sa'oi biyu da rabi bayan wannan tattaunawar sai ga fadar White House ta fitar da wata sanarwa cikin wasu shafuffuka dangane da tattaunawar wanda mafi yawan abin da aka fadi ba gaskiya ba ne.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Rubuta irin wannan sanarwar cikin sa'oi biyu ba abu ne mai yiyuwa ba. A saboda haka wadannan mutanen a daidai lokacin da suke tattaunawa da mu, a bayan fage kuma sun shagaltu da rubuta wata sanarwa ta yaudara da ke ciki da karya da ya saba wa abin da ake tattaunawar.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Wani misalin kuma shi ne cewa bayan duk wata tattaunawar da aka yi, su kan fito fili suna magana amma a bayan fage kuma suna (gaya mana) cewa suna fadin hakan ne saboda kiyaye mutumcinsu a cikin gida da kuma fuskantar ‘yan adawa na cikin gida ne. To mu dai hakan bai fashe mu ba.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Koda yake mu ma suna jingina hakan gare mu. Suna cewa mai yiyuwa ne bayan an cimma yarjejeniyar, Jagora ya zo ya yi adawa da hakan, don dai ya kare mutumcinsa.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Maganar da jagora yake yi da mutane ta ginu ne bisa yarda da juna. Kamar yadda mutane suka yarda da ni, ni ma na yarda da al'ummar Iran. A koda yaushe na yi amanna da cewa (taimakon) Allah yana tare da jama'a.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: Fitowar mutane cikin tsananin sanyin ranar 22 ga watan Bahman ko kuma cikin tsananin zafin watan Ramalana a ranar Kudus, dukkanin wadannan abubuwa ne da suke nuni da hannun Ubangiji. A saboda haka ne muna da cikakkiyar yarda da al'ummarmu. Maganar da muke da su ta ginu ne bisa wannan yarda da kuma gaskiya.
Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Lalle ni dai ina da shakku cikin irin halaye da dabi'un daya bangaren da ake tattaunawa da shi.
Haka nan kuma yayin da yake magana kan masu goyon baya da kuma adawa da abin da aka cimma a wajen tattaunawar a cikin Iran, Jagoran cewa yayi: Bai kamata a dinga kambama abubuwa dangane da wannan lamarin ba ko kuma gaggawa ba, face dai wajibi ne a yi hakuri a ga me zai faru a nan gaba.
Jagoran juyin juya halin Musulunci dai ya kirayi jami'an gwamnati da su yi wa mutane musamman masana bayanin abubuwan da suka faru a yayin tattaunawar, don mutane su san hakikanin abin da ya faru. Lalle mu ba mu da wani abin boyewa cikin lamarin.
Ayatullah Khamenei ya bayyana sanar da mutane halin da ake ciki da abubuwan da aka tattauna din a matsayin alama ta hadin kai da aiki tare tsakanin gwamnati da mutane da Jagoran yayi kiran da a same shi.
A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya gabatar da wata shawara ga jami'an gwamnati inda ya ce: Jami'an gwamnati, wadanda mutane ne masu gaskiya sannan kuma masu fatan alheri ga kasa, wajibi ne su kirayi masu sukan wannan tattaunawar su tattauna da su; idan har akwai wani abin da suka fadi (mai amfani) to su yi amfani wajen ciyar da tattaunawar gaba. Idan ma har babu, to su yi kokarin kwantar musu da hankali.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: Hakan alama ce ta aiki tare da kuma kusato da zukata waje guda.
Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Mai yiyuwa ne jami'an su ce saboda karancin lokaci sakamakon wa'adin watanni uku da aka tsara kafin cimma yarjejeniyar, don haka babu lokaci sosai da za a tattauna da kuma jin ra'ayin masu adawa. A nan ana iya cewa shi dai wannan wa'adi na watanni uku, ba wani wa'adi ne da ba za a iya sauya shi ba. Ko da an kara wannan wa'adin babu wata matsala kamar yadda a baya ma bangaren da ake tattaunawa da shi ya kara tsawon watanni bakwai din da aka diba.
A ci gaba da jawabin nasa, Ayatullah Khamenei ya sake jaddada cewar tattaunawar da ake yi da Amurka kan batun nukiliya ne kawai, ban da wani batun na daban, inda ya ce: Tabbas tattaunawar da ake yi kan nukiliya za ta iya zama wata jarabawa ce. Idan har bangaren da ake tattaunawa da shi din ya kauce wa irin wasa da hankali da karya alkawarin da ya saba yi. To ana iya sake gwada hakan a kan wasu batutuwan na daban. To amma matukar ya ci gaba da wannan wasa da hankalin, to kuwa hakan zai kara karfafa mana irin ra'ayinmu ne da kuma rashin yarda da Amurka da muke da shi ne.
Har ila yau kuma Ayatullah Khamenei ya nuna damuwarsa kan yadda wasu suke bayyana bangaren da ake tattaunawa da shi din da cewa ana fuskantar kasashen duniya ne inda ya ce: Daya bangaren da ke (tinkararmu) wanda kuma yake mummunar mu'amala da al'ummar Iran, Amurka ce da wasu kasashen Turai su uku, ba wai kasashen duniya ba. Kasashen duniya dai su ne kasashe 150 na duniya wadanda a 'yan shekarun baya shugabanni da manyan jami'ansu suka gudanar da taron kasashen 'yan ba ruwanmu a nan Tehran. Don haka abin da wasu suke cewa wai muna fada ne da kasashen duniya da wajibi ne mu nemi yardarsu, lalle ba haka lamarin yake ba.
Daga nan kuma sai Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayi karin haske kan abubuwan da yake gaya wa jami'an gwamnati a ganawar da suke yi a kebe dangane da batun nukiliyan inda ya ce: Ni dai ina kiran jami'an gwamnati da su dauki nasarorin da ya zuwa yanzu aka samu a matsayin wasu nasarori masu girma da kuma muhimmancin gaske. Kada su dauki hakan a matsayin wani lamari maras muhimmanci da kimar gaske.
Ayatullah Khamenei ya bayyana mallakar fasahar nukiliya a matsayin wata lalura da wajibi ne a samar da ita ga kasar Iran yana mai cewa: Abin da wasu masu da'awar sani suke fadi na cewa "me za ku yi da fasahar nukiliya" lalle wannan wata yaudara ce.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da bukatar da kasar Iran take da shi ga fasahar nukiliyan a fagagen samar da makamashi, magunguna, tace ruwan kogi da kuma ayyukan gona, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Mafi muhimmancin siffar da fasahar nukiliya na kasar nan take da shi, shi ne cewa an samu wannan fasahar ce albarkacin tsayin daka da kuma kokarin matasan kasar nan. A saboda haka wajibi ne a ci gaba da kiyaye ci gaban da ake da shi a wannan fagen.
har ila yau kuma yayin da yake magana kan ikirarin da wasu kasashe masu laifi irin su Amurka wacce ta taba amfani da makamin nukiliya ko kuma kasar Faransa wacce ta taba gudanar da wani gwaji mai matukar hatsarin gaske na nukiliya, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: Wadannan mutanen suna tuhumarmu da cewa muna son kera makamin nukiliya, alhali kuwa gwamnatin musulunci ta Iran, bisa fatawa ta shari'a haka nan kuma bisa dogaro da hankalinta, ba ta taba neman kera makamin nukiliya ba, kuma a nan gaba ma ba za ta yi hakan ba. Tana ganin hakan a matsayin wani lamari mai wahalarwa da kuma cutarwa.
Kira na biyu da Ayatullah Khamenei yayi wa jami'an gwamnatin shi ne kada su yarda da sakin fuskar da Amurkawa suke musu inda ya ce: A baya-bayan nan daya daga cikin jami'an gwamnatin Iran a fili ya fadi cewa mu dai ba mu yarda da kuma samun kwanciyar hankali da daya bangaren da muke tattaunawar ba. Lalle irin wannan matsaya, matsaya ce mai kyau.
Ayatullah Khamenei dai ya ce bai kamata jami'an gwamnati su yaudaru da sakin fuska da dariyar da Amurkawa suke musu ba da kuma sakankancewa da alkawurran da suka yi ba, inda ya ce: Babban misalin hakan shi ne matsaya da kuma jawabin da shugaban Amurka yayi bayan sanarwar cimma wata yarjejeniyar da aka yi.
Dage dukkanin takunkumin da aka sanya wa Iran shi ne batu na gaba da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi jami'an na Iran da su yi la'akari da shi yayin tattaunawar inda ya ce: Lalle wannan batu ne mai matukar muhimmanci. Wajibi ne a dage dukkanin takunkumin da aka sanya wa Iran a daidai ranar da aka cimma wannan yarjejeniyar.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Idan har ya zamana za a damfara dage takunkumin da wani batu na daban, to kuwa tushen tattaunawar zai zamanto ba shi da wata ma'ana kenan. Don kuwa manufar tattaunawar ita ce dage takunkumin.
Batu na gaba da Ayatullah Khamenei yayi ishara da shi, shi ne batun masu bincike da sanya ido inda ya ce: Ta kowace fuska bai kamata a bari a keta hurumin tsaron kasa ba ta hanyar fakewa da batun sanya ido. Haka nan kuma jami'an sojin kasar nan ta kowace fuska ba su da damar da za su bude kofa ga 'yan kasashen waje saboda fakewa da batun bincike ko kuma su dakatar da irin fadada karfin kariya da ake da shi a kasar nan.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Wajibi ne irin karfin kare kasa da ake da shi ya ci gaba da zama hakan, sannan kuma a kowace rana ma a dinga karawa da karfafa shi. kamar yadda kuma ta kowace fuska yayin tattaunawar a rage kaifin irin goyon bayan da ake ba wa 'yan'uwanmu 'yan gwagwarma a yankuna daban-daban ba.
Dangane da batun yadda za a gudanar da bincike da sanya idon kuwa Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana hanyoyin da suka dace a bi inda ya ce: Ba za a taba amincewa da sanya ido da bincike da ya saba da yadda ake gudanarwa da shi ba, ta yadda za a mayar da Iran wata kasa ta musamman a wannan fagen. Wajibi ne sanya idon ya zamanto irin sanya idon da aka saba da shi da ake gudanar da shi a duk fadin duniya. Ban da sama da haka.
Tunatarwa ta karshe da Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi shi ne kan wajibci ci gaba da nasarori da fadada ayyukan da aka samu cikin shirin nukiliyan na Iran.
Jagoran ya ce: Wajibi ne a ci gaba da fadada wannan aiki da ake yi a dukkanin fagage. Koda yake mai yiyuwa ne masu tattaunawar su ga cewa ya zama wajibi su amince da 'yan wasu iyakancewa. Ni dai ba ni da cewa a wannan bangaren. To amma dai wajibi ne a ci gaba da shirin fadada irin nasarorin da aka samu.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Tabbatar da wadannan bukatu yana wuyan masu tattaunawar ne. Suna iya amfani da ra'ayuyyukan masana amintattu da kuma masu suka wajen tsara hanyar da ta dace wajen tattaunawar.
A ci gaba da jawabin nasa, Ayatullah Khamenei yayi ishara da lamari mai muhimmancin gaske na abin da ke faruwa a kasar Yemen inda ya ce: Saudiyyawa sun tafka kuskure sakamakon harin wuce gona da iri da suke kai wa kasar Yemen sannan sun kirkiro wata mummunar bidi'a a wannan yankin.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kwatanta abubuwan da gwamnatin Saudiyyan take yi a Yemen a halin yanzu da irin danyen aikin da sahyoniyawa suke yi a Gaza daga nan sai ya ci gaba da karin haske kan wannan lamarin.
Har ila yau Ayatullah Khamenei ya bayyana hare-haren da gwamnatin Saudiyyan take kai wa Yemen a matsayin wani laifi na yaki da kisan kiyashi da za hukumta mai aikata shi, inda ya ce: Kashe kananan yara, rusa gidaje da kuma ruguza tushen tattalin arzikin wata kasar, babban laifi ne.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Ko shakka babu Saudiyyawa ne za su cutu cikin wannan lamari, sannan kuma babu ta kanda za su yi nasara.
Ayatullah Khamenei ya bayyana dalilinsa na cewa lalle Saudiyyawan za su sha kashi a wannan yakin da cewa: Dalilin hakan kuwa a fili yake. Don kuwa karfi na soji da Sahyoniyawa suke da shi ya ninninka na Saudiyya sannan kuma Zirin Gaza wani dan karamin yanki ne, to amma sun gagara samun nasara a Gazan. Alhali kasar Yemen, wata kasa ce mai girma da ke da miliyoyin mutane.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Ko shakka babu Saudiyya za su cutu cikin wannan lamarin, sannan kuma za a turbude hancinsu a cikin kasa.
Yayin da kuma yake magana kan siyasar wajen kasar Saudiyyan, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: Lalle muna da sabani na siyasa kala-kala da kasar Saudiyya, to amma a kullum mu kan gaya musu su yi amfani da kula da sanin ya kamata cikin siyasarsu ta waje. To amma sun bari wasu samaruka marasa kwarewa sun rike harkokin gudanar da kasar da kuma fifita bangaren dabbanci da son amfani da karfi a kan bangaren amfani da hankali da sanin ya kamata. wanda ko shakka babu hakan cutarwa ce a gare su.
Daga nan sai Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kirayi gwamnatin Saudiyyan da cewa: Wannan abin da kuke yi a yankin nan ba abu ne da za a amince da shi ba. Don haka ina jan kunnenku da ku dakatar da wannan danyen aiki da kuke yi a Yemen.
Daga nan kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi magana ne dangane da irin goyon bayan da Amurka take ba wa gwamnatin Saudiyya cikin wannan danyen aikin inda ya ce: wannan dai it ace dabi'ar Amurka, wacce a dukkanin lamurra maimakon ta goyi bayan wadanda ake zalunta, sai ta koma tana goyon bayan azzalumi. To amma a wannan lamarin su ma za su cutu sannan kuma za su sha kashi.
yayin da yake magana kan ikirarin da ake yi na tsoma bakin Iran cikin harkokin kasar Yemen, Ayatullah Khamenei cewa yayi: Jiragen yakinsu suna nan suna ta kai hare-hare kasar Yemen suna masu fakewa da wasu dalilai na wauta da babu wanda zai yarda da shi. Ba sa ganin hakan a matsayin tsoma baki, amma suna tuhumar Iran da tsoma baki cikin harkokin kasar Yemen.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana al'ummar Yemen a matsayin wata al'umma ma'abociyar kwarewa da kuma karfin ayyana irin gwamnatin da suke, don haka ya sake jaddada cewa: Wajibi ne Saudiyya ta gaggauta dakatar da wannan danyen aiki nata.
Jagoran juyin juya halin Musulunci dai ya ce tsarin da makiya al'ummar Yemen din suka tsara tun farko shi ne samar da rikici da yake yake irin wanda suka haifar a kasar Libiya inda ya ce: Abin farin cikin shi ne cewa sun gaza wajen cimma wannan manufar. Don kuwa matasan kasar wadanda suka yi amanna da tafarkin mai girma Amirul Muminin Ali (a.s) da suka hada da Shi'a da Sunna, da Zaidiyawa da Hanafawa sun tsaya kyam. A nan gaba ma za su ci gaba da wannan tsayin dakan har su sami nasara.
3112981