Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ghana Web cewa, wannan cibiyar mata musulmi a kasar Ghana za ta shirin gudanar da waninanshiri ne na musamamn domin bayar da horo ga mata kan shugabanci da kuma rawar da za su taka a wannan bangare.
Mariyama Aubang it ace shugabar kungiyar hadin kan mata musulmi akasar ta Ghana, ta bayyana cewa bababr manufarsu ta daukar wannan aniya domin gudanar da wannan horo ga matai ta ce, suna son su wayar da kan matan ne ta yadda za su gane matsayinsu a mulsunce kan batutuwa da suka shafi tafiyar da lamurran jama’a.
Ta ci gaba da cewa idan aka yi maganar shugabcni hakan na nufin yadda za su iya tafiyar da lamurra atsakaninsu s kansu mata, a siyance da kuma sauran harkoki nay au da kullum, ta yadda mace za ta iya yin abin da ya kamata a wanann bangare tare da amfanar da yan uwanta mata ba tare da wata matsala ba.
Yanzu haka dai a cewarta mata da ma ne suka bayyana sha’arsu ta shiga cikin shirin domin kada a barsu a baya, ta yadda za su iya taka rawa domin ci gaban al’ummarsu musamamn ma musulmi mata a cikin kasarsu, wanda kuma hakan shi ne burin wannan horo.
3140667