IQNA

Musulmin Kasar Faransa Na Bukatar Manyan Masallatai A Kasa

22:49 - April 16, 2015
Lambar Labari: 3157561
Bangaren kasa da kasa, Dalil Bubakar shugaban masallaLille na kasar Faransa ya bayyana cewa suna da bukatr manyan massalatai a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na France3 cewa, bayan da Dalil Bubakar ya gabatar da wanann bukata Umar Lisfar shugaban kungiyar musulmi ta kasar (UOIF) ya bayyana cewa wanann babbar magana ce ya kamata a bayar da hankali a kanta.
Lisqar ya sheda wa tahashr Eurpe 1 cewa,  halin yanzu akwai masallatai 2200, kuma a cewarsa wadanan masallatai za su ninka har sau biyu a cikin shekaru biyu masu zuwa, kuma suna daukar mutane 100 ne kawai, wanda kuma akwai bukatar kari.
Shi ma a makon da ya gabata Dalil Bubakar ya ce gaba da cewa a halin yanzua kwai musulmi da adadadinsu ya kai miliyan bakwai  a cikin kasar kuma wannan adadin masallatai dubu biyu da dari uku ba zai ishe sub a domin gudanar da harkokinsu na addini ba tare da takura ba.
A bangare guda kuma ya kara da cewa yanzu haka dai suna cikin bin kadun wanann lamari, bisa la’akari da cewa yana bukatar da namijin kokari kafin cimma wannan buri bai yi karin haske danagne da hanyoyin da zai bi domin samun kudin gina masallatan ba da kuma lokacin samunsu.
3106595

Abubuwan Da Ya Shafa: faransa
captcha