IQNA

Babban sakataren majalisar dinkin Duniya Ya bukaci Kawo Karshen Rikicin Yemen

23:47 - April 17, 2015
Lambar Labari: 3162661
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren majalisar dinkin duniya ya bukaci dukkanin bangarorin rikici a kasar da su gaggauta kawo karshen yaki tare da dakatar da bude wuta nan take.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Dar-Alhayat cewa, tun bayan da Saudiyya ta fara kaddamar da hare-haren kisan gilla kan al’ummar yemen a karon farko Ban Ki Moon babban sakataren majalisar dinkin duniya ya bukaci dukkanin bangarorin rikici a kasar da su gaggauta kawo karshen yaki tare da dakatar da bude wuta ba tare da wani bata lokaci ba.

Ban Ki Moon y ace yakin da yake faruwa a halin yanzu a cikin kasar Yemen yana cutar da fararen hula da ba su da wata alaka da lamarin, bil hasali ma su ne ake ta kashewa, a kan babu dalilin ci gaba da wannan yaki, ya zama  wajibi a kawo karshensa ba tare da wani bata lokaci ba.

Wata Cibiyar fafatukar kare hakkin bil-Adama mai zaman kanta a kasar Yeman ta sanar da cewar yawan mutanen da hare-haren wuce gona da irin kasar Saudiyya suka kashe a kasar ta Yeman sun doshi dubu biyu da dari shida.

Shugaban Cibiyar kare hakkin bil-Adama da ke kasar Yeman ya bayyana cewa tun daga lokacin da jiragen saman yakin kawancen kasashen Larabawa da Amurka karkashin jagorancin kasar Saudiyya suka fara kai hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yeman a ranar ashirin da shida ga watan Maris zuwa jiya Alhamis sha shida ga watan Aprilu sun yi sanadiyyar kashe mutane dubu biyu da dari biyar da casein da shida yayin da mutanen da suka jikkata suka haura zuwa  kusa dubu hudu.

Ya kara da cewa; kididdiga ta tabbatar dacewar daga cikin mutanen da suka rasa rayukansu, dari uku da casein da shida kananan yara ne, yayin da yawan mata suka kai dari biyu da hasin da biyar.  

3159602

Abubuwan Da Ya Shafa: Moon
captcha