IQNA

Wani Musulmin Amurka Na Shirin Tafiya Jahohi 50 Domin Isar Da Musulunci

23:54 - April 18, 2015
Lambar Labari: 3169190
Bangaren kasa da kasa, wani musulmin kasar Amurka daga jahar Machigan na shirin gudanar da wata tafiya zuwa jahohi 50 daga cikin jahohin kasa domin isar musu da sakon musulunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na IINA cewa, Jamil Sayyid musulmin kasar Amurka daga jahar Machigan ya fara gudanar da wata tafiya zuwa jahohi 50 daga cikin jahohin kasar ta Amurka domin isar musu da sakon musulunci na manzon (SAW) na hakika maimakon irin masaniyar da suke da ita.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan tafiya ta tsawon kwanaki 35 ta fara ne daga Hawaii, kuma zai ci gaba da tafiya yana safka a masallatai na jahohin da zai ziyarta inda zai kamala a wani masallaci da ke cikin jahar Michigan.
Wanann mutum mai shekaru 40 ya yi karatu a jami'ar Michigan, kuma yana da burin ganin cewa ya isar da sakon muslunci ga sauran al'ummomin da suka jahilci wanann addini mai girma, kuma yake kokarin fahimtar da su abin da suka jahilta dangane da shi.
Tuni dai ya fara isar da sakonsa kamar yadda ya tsara , kuma yan asamun karbuwa daga dukaknin mutanen da yake haduwa da su a cikin tafiyar tasa.
3165889

Abubuwan Da Ya Shafa: musulmi
captcha