IQNA

Ku Kara Shiri Na Tsaro Da Kariya Wannan Lamari Ne Da Ya zama wajibi A Kanku

23:20 - April 19, 2015
Lambar Labari: 3175675
Bangaren siyasa, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei jagoran juyin juya halin muslunci a lokacin ganawarsa da manyan jami’an soji da kuma na ma’aikatar tsaro a yau ya bayyana cewa, dole ne a kara mayar da himma wajen bunkasa ayyukan tsaro da kare kasa domin zama cikin shiri da fusantar kowane irin kalu bale.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na shafin jagora cewa, a yau Lahadi 19-04-2015 ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da manyan kwamandoji, jami'ai da iyalan shahidan soji na Iran inda ya kirayi sojojin na Iran da su ba da himma wajen kiyaye da kuma karfafa basira da kuma irin karfi na kariya da suke da su. Jagoran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta taba zama barazana ga wannan yanki da kuma kasashen da suke makwantaka da ita ba, a nan gaba ma ba za ta zama ba. To mma kuma za ta mayar da martani da dukkan karfinta ga duk wani kokarin wuce gona da iri a kanta.
A yayin wannan ganawar wacce aka yi ta don tunawa da ranar sojojin kasa na Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci kuma babban kwamandan sojojin na Iran ya taya sojojin murnar wannan rana ta sojojin, inda ya bayyana sanya wa ranar 29 ga watan Farvardin sunan ranar sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayin daya daga cikin manyan ayyukan da marigayi Imam Khumaini (r.a) yayi a farko farkon nasarar juyin juya halin Musulunci don kawo karshen kokarin da wasu suke yi na kawar da sojojin na Iran. Jagoran ya ci gaba da cewa: Sakamakon hikima da hangen nesan marigayi Imam Khumaini (r.a) ne sojojin Iran suka ci gaba da zama kyam da karfinsu, sannan kuma suka taka rawar da ya dace a matsayinsu na wata cibiya ta juyin juya halin Musulunci ciki kuwa har da rawar da suka taka a lokacin kallafaffen yaki na shekaru takwas.
Har ila yau kuma yayin da yake bayyana ranar 29 ga watan Farvardin a matsayin wata alama ta tsayin dakan sojojin Iran wajen kare juyin juya halin Musulunci da kuma manufofin al'umma, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa yayi: Daya daga cikin manyan siffofin da sojojin Iran suka kebanta da su, ita ce riko da kuma kiyaye koyarwa ta addini.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da rashin kula da kuma kiyaye dokokin kasa da kasa da kuma koyarwa ta dan'adamtaka da mafi yawa daga cikin sojojin duniya suke yi a yayin nasara ko kashin da suka sha, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: Babbar misalin hakan, shi ne dabi'u da mu'amalar sojojin manyan kasashen duniya musamman Amurka wadanda babu ruwansu da komai kashin girmama dokokin kasa da kasa da koyarwar bil'adama. Face ma dai suna aikata kowane irin mugun abu.
Jagoran ya bayyana abin da ke faruwa a Yemen, da kuma abubuwan da suka faru a lokacin yakin Gaza da Labanon a matsayin misalan rashin kula da kiyaye dokokin kasa da kasa da ake yi inda ya ce: A koda yaushe sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun kasance masu kula da kuma kiyaye dokokin da koyarwar Musulunci. Sannan kuma babu wani lokaci, shin lokacin da suka sami nasara ne da suke nuna girman kai da dagawa, kamar yadda kuma ba sa amfani da wasu hanyoyi da aka haramta a lokacin da suke cikin hatsari.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Sanarwar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi na cewa ba ta nufin kera makaman nukiliya, ta ginu ne bisa wannan tsari da kuma koyarwa ta Musulunci ne.
Yayin da kuma yake magana da kuma yin watsi da farfagandar da wasu suke yadawa na cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana tsoma baki cikin harkokin cikin gida wasu kasashen yankin nan, Ayatullah Khamenei cewa yayi: Wannan tuhuma ce maras tushe. Don kuwa Iran ba ta tsoma baki cikin harkokin cikin gidan wasu kasashe, kuma a nan gaba ma ba za ta yi ba.
Jagora ya ce: Mu dai muna kyamar mutanen da suke kai hare-hare ga fararen hula, mata da kananan yara, sannan kuma mun yi amanna da cewa su din nan sun yi nisa da koyarwar Musulunci da kuma lamiri na dan'adam. To amma lalle ba ma tsoma baki cikin harkokin cikin gidan wasu kasashe.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana riko da koyarwar Musulunci da kuma girmama dokokin kasa da kasa da sojojin Iran suke yi a matsayin babban dalilin da ya sanya suka zamanto abin kaunar zukatan al'umma inda ya ce: Wata siffar ta daban da sojojin Iran suka kebanta da ita, ita ce kara irin karfi da shirin da suke da shi na kariya da makamai, wanda hakan yayi daidai da koyarwar ayar nan ta Alkur'ani mai girma da take cewa: "Kuma ku tanadi karfi dominsu gwargwadon iyawanku".
Ayatullah Khamenei ya bayyana irin ci gaban da sojojin na Iran suka samu a bangaren makamai da dabarun kariya a matsayin wani ci gaba mai girman gaske kuma abin kwatance, daga nan sai ya ce: Dukkanin wadannan nasarori da karfin da aka samu, an same su ne a daidai lokacin da kasar nan take cikin matsin lamba da takunkumi, wanda hakan wani aiki ne mai girman gaske. Don haka wajibi ne a ci gaba da irin wannan aikin.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da fushi da bakin cikin da makiyan al'ummar Iran suke ciki saboda irin wannan ci gaba na kariya da sojojin na Iran suka samu, sannan da kuma kokarin da suke yi wajen ganin sun yi kafar ungulu ga hakan, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: A saboda haka ne suka kara matsin kaimi da kuma kara farfaganda kan wannan lamarin musamman kan irin ci gaban da ake samu a fagen makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuka. To amma abin da ya dace shi ne riko da wannan aya mai girma ta Alkur'ani da take cewa mu ci gaba da riko da wannan tafarki na ci gaba da tanadi din da dukkan karfinmu.
Har ila yau kuma yayin da yake ishara da barazanar rashin mafadi da Amurka take yi wa Iran, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: Bayan shirun na dan wani lokaci da suka yi, sai ga shi a baya-bayan nan daya daga cikin jami'ansu ya sake maganar batun hari da amfani da karfin soji. A bangare guda wadannan mutane suna barazana, sannan a bangaren guda kuma suna cewa wajibi ne Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dakatar da irin ci gaban da take samu a bangaren kare kasa. Lalle magana ce ta wauta.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Koda wasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba amincewa da wannan magana ta wauta ba. Al'ummar Iran dai sun tabbatar da cewa a duk lokacin da suka fuskanci wani wuce gona da iri, to kuwa za su kare kansu da dukkan karfinsu. Sannan kuma za su hada hannunsu waje guda wajen buge hancin duk wani mai wuce gona da iri maras hankali.
Yayin da ya koma kan sojojin kuwa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin kuma babban kwamandan sojojin na Iran ya gaya musu cewa: Wajibi ne dukkanin cibiyoyin soji da suka hada da ma'aikatar tsaro da sojoji da dakarun kare juyin juya halin Musulunci su ci gaba da karfafa dukkanin karfi da shirin da suke da shi na soji da na kariya a dukkanin fagage. Hakan kuwa wani umurni ne a hukumance.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran, duk da irin karfi na kariya da na soji da take da shi, to amma ba za ta taba zama barazana ga wannan yankin da kuma kasashen da suke makwabtaka da ita ba.
Haka nan kuma yayin da yake magana kan zuki da mallen Amurka da wasu kasashen Turai da ‘yan amshin shatansu na cewa Iran tana kokarin mallakan makaman nukiliya da kuma bayyana Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayin wata barazana, Ayatullah Khamenei cewa yayi: A halin yanzu dai babbar barazana ga duniya da kuma wannan yankin, Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila ne, wadanda ba tare da kiyaye duk wata doka ta kasa da kasa ko kuma ta dan'adamtaka ba suke tsoma baki da kai hare-hare ga duk inda suke so da kuma zubar da jinin mutane.
Jagoran ya bayyana hare-haren wuce gona da irin da ake kai wa kasar Yemen bisa goyon bayan Amurka da kasashen yammaci da kuma ba da kariya ga masu wuce gona da irin a matsayin daya daga cikin misalan irin dabi'un wadannan mutanen da suke barazana ga tsaron duniya, daga nan sai ya ce: Jamhuriyar Musulunci ta Iran, sabanin wadancan masu tinkaho da karfi, tana ganin tsaro a matsayin mafi girman ni'ima ta Ubangiji, sannan kuma ta tsaya kyam wajen kare tsaron kanta da kuma na wasu.
A karshen jawabin nasa dai, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada cewa: Kiyaye tsaron kasa, kan iyakoki da kuma rayuwar yau da kullum ta al'umma daya ne daga cikin mafiya muhimmancin nauyin da ke wutan jami'an gwamnati da kuma na soji.
Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musulunci sai da babban hafsan hafsoshin sojin na Iran Manjo Janar Salehi ya gabatar da jawabinsa inda yayin da yake magana kan ranar 29 ga watan Farvardin, wato ranar sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, cewa yayi: Sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ma'abota riko da juyin juya halin Musulunci na kasar suna cikin shirin da ya kamata wajen kare kan iyayoyi da kuma mutumci da manufofin kasar Iran.
Manjo Janar Salehi, ya ci gaba da cewa: "Babban abin da sojojin Iran suka sa a gaba, ba tare da la'akari da amincewa ko rashin amincewar wasu ba, shi ne daukakarsu da kuma kasarsu. Sannan kuma a shirye suke cikin kowane irin yanayi su sake bayyanar da irin kwarewa da karfin da suke da shi.
3172363

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha