IQNA

Kokarin Rauna Gwagwarmaya Ne Ya Sanya Ake Ci Gaba Da Kai Harin Yemen

23:52 - April 22, 2015
Lambar Labari: 3194131
Bangaren kasa da kasa, a wani taro da suka gudanar a birnin Beirut na kasar Lebanon gugun malamai masu goyon bayan gwagwarmaya sun bayyana hari kan Yemen da cewa hankoro ne na neman raunana gwagwarmaya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Saba'a Net cewa, gugun malamai masu goyon bayan gwagwarmaya sun bayyana hari kan Yemen da cewa hankoro ne na neman raunana gwagwarmayar al'umma.
Bayanin ya ci gaba da cewa dangane da batun dakatar da bude kuwa masana da dama suna ganin cewa batun dakatar da yakin ba hannun Saudiyyah yake ba, domin tun asali yakin ba nata ba ne, yaki ne na Amurka da yahudawa take aiwatar musu, kuma hakan na daya daga cikin shirinsu na rusa kasashen musulmi da na larabawa.
Wanda kuma masarautar Al saud da turawan mulkin mallaka suka kafa tare da mika mata dukkanin madafun iko a hijaz wadda turawan suka mayar Saudiyyah ta yanzu, ita ce babban makamin da suke amfani da shi a halin yanzu domin aiwatar da wannan shiri nasu na rusa kasashen musulmi da na larabawa, kama da irin rawar da masarautar ta taka wajen rusa wasu kasashen da kuma Yemen a halin yanzu.
A nasu bangaren kuma masana kan harkokin tsaro da ayyukan soji suna ganin cewa masarautar Al Saud ba ta iya cimma  ko daya daga cikin manufofin kaddamar da yakin ba da ta shelanta tun daga farko, domin kuwa ba iya kawarda ko murkushe kungiyar huthi ba, haka nan kuma ba ta iya dawo da yaronta kan mulkin kasar ta Yemen ba.
Amma amma ta samu gagarumar nasara wajen kashe fararen hula fiye da  dari daya  da suka hada da mata da kananan yara da tsoffi, tare da mayar da daruruwan yara marayu, da kuma rusa cibiyoyin ilimi da masallatai, da gadojin da suka hada manyan biranan kasar, kamar yadda ta samu nasara wajen rusa cibiyoyin wutar lantarki da na iskar gas da kuma asibitoci, gami da dubban gidajen jama'a.
3183327

Abubuwan Da Ya Shafa: lebanon
captcha