Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Manarah cewa, wadannan kwafin kur'anai an mika su gay an darikar a matsayin kyauta daga babbar cibiyar sarki Muhammad na shida.
Ofishin jakadancin kasar Morocco a birnin Dakar fadar mulkin kasar Senegal ne ya mika wadannan kwafin kur'anai ga shugaban darikar ta kadiriyyah haji Bu Muhammad Kunta, da nufin raba su ga dukkanin mabiyansa da ke kasar.
Cibiyar sarki na Morocco dai na ke kokarin nuna cewa yana tare da dukaknin bangarori na mabiya darikun sufayea cikin kasar ta Senegal da ma dukkanin yankunan yammaci da arewacin nahiyar, ta hanyar buga wasu abubuwa irin wadannan da kuma raba su gare su.
Kafin wanann lokacin ita wnann cibiya ta dauki raba wasu kwafin kura;anai da kuma wasu kyautuka mabiya darikar sufanci na Mudiyyah da ke garin taubah, birni na biyu mafi girma a kasar ta Senegal, wanda hakan kan ba sarkin karbuwa atsakaninsu.
3204808