Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alomanama Post cewa, Sheikh Muhammad Almansi wanda shi daya ne daga cikin mambobin majalisar malaman addinin muslunci na mazhabar ahlul bait (AS) a Bahrain ya bayyana a taron da jam’iyyar Alwifaq ta shirya cewa nuna banbancin da ake yi wa ‘yan shi’a a kasar ya samo asali ne tun tsawon tarihi.
Sheikh Muhammad Almansi ya ci gaba da cewa tun bayan da aka kafa kasar tare da mika ta ga bangaren da ke mulki nay an sunna da turawa suka yi, an mayar da mabiya mazhabar Ahlul bait (AS) saniyar warea cikin komai, kama daga batun tafiyar da lamurra a kasar, da kuma daidaita su da sauran ‘yan kasa mabiya wasu mazhabobin na daban.
Ya ci gaba da cewa duk da cewa mabiya mazhabarshi’a kusan daukacin mutanen kasar, amma kuma har yanzu ba a san da zamansu a hukumance ba ta fuskar karatu, ta yadda mabiya mazhabar shi’a dole ne su salon karatu na sunna a dukkanin makarantun gwamnatin kasar matukar dai suna son su yi karatu.
Malamin ya kara da cewa danne hakkokinsu da ake yi bai tsaya kan batun nuna musu wariya ta fuskar karatu ba kawai, har ma ta fuskar siyasa kasar, ta yadda an sanya tsarin da bai yarda da al’ummar kasa su zama suna da hannu a cikin lamrin tafiyarwa ba, matukar ba su cikin gidan da ke sarauta, ko kuma masu yi musu hidima daidai da manufofinsu.
Abubuwan da suke faruwa yanzu a kasar ta Bahrain dai sun isa s zama babban daily na irin wariyar da ake nuna wa mabiya mazhabar shi’a a kasar.
3215638