IQNA

Shugaban Senegal Ya Jadda Muhimmancin Kafofin Sadarwa Wajen Yada Addinin

21:04 - April 29, 2015
Lambar Labari: 3231794
Bangaren kasa da kasa, Macky Sall Shugaban kasar Senegal ya bayyana cewa kafofin yada labarai na kasashen musulmi za su iya bayyana wa sauran al'ummomin duniya irin ta addinin musulunci.

Kamfanin dillancin labaran Iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, Macky Sall Shugaban kasar Senegal ya bayyana a gaban taron kasashen musulmi da ake gudanarwa a birnin Dakar fadar mulkin kasar cewa, kafofin yada labarai na kasashen musulmi za su iya taka gagarumar rawa, wajen bayyana wa sauran al'ummomin duniya kyakkyawar koyarwa irin ta addinin musulunci ga bil adama baki daya.
Ya ci gaba da cewa dole ne musulmi su mike baki daya, kowa ya bayar da irin gudunmawar da zai iya bayarwa domin tsamo wanann addini wanda ya shiga cikin tsangwama a duniya, sakamakon wasu ayyka na daban da ake aikatawa da sunasa, wanda kuma addinin muslunci bas hi da wata alaka da su.
Shugaban na Senegal yace yanzu akwai batutuwa da dama da ya kamata a ce musulmi sun mayar da hankalia  akansu, wadanda kuma hakan ba zai yiwu ba sai da kokarin kafofin yada labarai na kasashen msuulmi, wajen bayar da hankali ga wayar da kan al’ummomin duniya dangane da musulunci na gaskiya.
Ya ce ya zama wajibi a fito da hakikanin sura ta muslunci ga sauran al’umomin duniya da suke kallon muslunci a matsayin addinin ta’addanci da tashin hankaii, haka nan kuma ta hanyar kafofin yada labarai za a iya bayyana wa duniya halin da al’ummar palastine ke ciki da kuma yadda za a taimaka musu.
A taron na jiya an tattauna batutuwa da dama da suke da alaka da kasashen msuulmi, da hakan ya hada da batun raya a la’adu tsakanin wadannan kasashen, da kuma karfafa harkokin sadarwa da yada labarai ta hanyoyi na zamai, yadda za su isa ga sauran al’ummomi na duniya, kuma su bayyana sakonninsu cikin sauki.
Taron ya samu halartar wakilai daga dukaknin kasashe mambo a wannan kungiya ta kasashen musulmi a kwamitin raya al’adu da kafofin sadarwa na kungiyar.
3228651

Abubuwan Da Ya Shafa: senegal
captcha