IQNA

ISESCO Ta Yi Kira Zuwa Ga Kawo Karshen Fitintinu A Tsakanin Musulmi

19:38 - May 04, 2015
Lambar Labari: 3255031
Bangaren kasa da kasa, kungiyar bunkasa harkokin ilmi da aladun kasashen musulmi ta ISESCO a taron cika shekaru 33 da kafa kungiyar ta yi kira zuwqa ga kawo karshen fitintunan banbancin fahimta atsakanin musulmi.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ISESCO cewa, kungiyar a ranar cika shekaru 33 da kafata ta yi kira ga dukkanin bangarori na maboya addinin muslunci, da su kawo karshen fitintunan banbancin fahimta a tsakaninsu tare da yin sulhu da fahimtar juna.

Bayanin wanda shi ne irinsa na farko da kungiyar ta fitar tun bayan da kasashen da suke hankoron haifar da fitina tsakanin al’ummar musulmi suka shelanta yaki kan wasu daga cikin kasashen yankiin da sunan banbancin mazhaba ko fahimta, ya zo ne da nufin kara rage kaifin fitinar da ke faruwa a yankin.

Kungiyar ta ce babu wani dalili da zai sanya musulmi su ki ahada kai domin fuskantar abin da ke gabansu na ilmantar da musulmi kan sahihin addini, tare da mayar da hankali ga barazanar da musulunci ke fuskanta a ciki da waje, maimakon tsayawa suina kafirta juna da zagin juna saboda banbancin fahimta kan wasu masaloli da ba su ne asalin addini ba.

Daga karshe kungiyar ta ce za ta mayar da hankali wajen ganin an samu daidaiton fahimta tsakanin dukkanin mabiya mazhabobi na musulunci domin samun hadin kai, kuma ta ce za ta ci gaba da yin iyaacion kokari domin ganin an cimma wannan manufa ta hada musulmi su zama sun fuskanci abin da ke ganasu.

Ga alama dai da wuyta wannan haka ta cimma ruwa domin kuwa kasashen da suke da hannu wajen rarraba kan al’ummar musulmi suna yin haka ne domin biyan bukatar makiya musluncin, wadanda kuma bna za su iya saba musuu ba.

3252716

Abubuwan Da Ya Shafa: isesco
captcha