IQNA

Za A Gina Masallacin da ya kebantanci Mata Zalla A Kasar Birtaniya

19:50 - May 04, 2015
Lambar Labari: 3255032
Bangaren kasa da kasa, ana shirin gina wani masallaci wanda ya kebanci mata zalla a kasar Birtaniya da nufin samar da wuri da zai basu damar gudnar da harokokinsu na addini.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na (Telegraph & Argus) cewa, manufar yin hakan it ace samar da wuri da ya shafi mata musulmi su kadai domin gudanar da lamurransu.

Bana Gura it ace shugabar majalisar mata musulmia  kasar Birtaniya ta bayyana cewa, suna da nufin yin hakane tare da tafiyar da wurin karkashin kulawar mata musulmi, wanda hakan zai ba su cikkiyar dam aba tare da wani ya yi musu katsalandan cikin harkokinsu na addini.

Ta kara da cewa sun yanke wannan shawara ne bisa la’akari da cewa dukaknin masallatan da suke cikin kasar Birtaniya ba su wadatarwa wajen warware matsaloli da dama da suka shafi mata, domin kuwa  a kowane lokaci mata suna da matsaloli da suke bukatar bayani a kansu, kuma samar da wuri na musamman zai taimaka musu a kan hakan.

Bayanin nata ya kara da cewa an gudana r irin wannan shiri a wasu kasashen an turai, kuma an ga amfaninsa matuka, saboda haka su ma ba aza a bar su a bay aba, tare da fatan na ba da jimawa ba za a samu asallacin mata na farko a kasar.

An dai gudanar da irin wannan shiri a birnin Los Angeles na kasar Amurka inda aka bude masallacin mata zalla  farkon wannan shekara, haka nan kuma a kasashen China, Chile, da kuma India.

3252688

Abubuwan Da Ya Shafa: birtaniya
captcha