Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, Sheikh Muhammad Yazbak ya bayyana cewar hatsarin ‘yan takfiriyya masu kafirta musulmi ya isa zuwa kasashen da suka kirkiro su da turo su zuwa kasashen yankin Gabas ta tsakiya, yana mai kira al’ummar musulmi da su hada karfi da karfe wajen fada da wadannan mutanen.
A wani jawabi da ya gabatar a yammacin yau wajen bikin maulidin Annabi da makon hadin kai da aka gudanar a kasar ta Labanon inda ya ce ‘yan takfiriyyan suna ci gaba da bata sunan Musulunci da Manzon Allah da sauran Annabawa da Manzannin Allah ta hanyar ayyukan da suke aikatawa da suka hada da zubar da jinin mutanen da ba su ci ba su sha ba.
Ya kara da cewa cutarwar da wadannan kungiyoyi suke yi wa Musulunci ba shi da tamka cikin tarihi. Don haka ya ce wajibi ne al’ummar musulmi da dukkanin mazhabobinsu su hada hannu waje guda wajen fada da wadannan mutanen.
A wani bangare na jawabin nasa, yayi kakkausar suka ga gwamnatin ahrain saboda irin zaluncin da take yi wa al’ummar kasar da suka fito don neman hakkinsu.