IQNA

20:25 - May 07, 2015
Lambar Labari: 3269146
Bangaren siyasa, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei dangane da barazanar da wasu jami’an Amurka biyu suka yi kan Iran ya bayyana cewa, tattaunawa karkashin barazana ba ta da wata ma’ana, Iran ba za ta amince da haka ba.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin jagora cewa, a safiyar Laraba 06-05-2015 ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da minister da manyan jami'ai da daraktocin Ma'aikatar ilimi da tarbiyya bugu da kari kan wani adadi mai yawa na malaman makarantun firamare da sakandare na kasar Iran don tunawa da zagayowar Ranar Malaman Makarantu na Iran don tunawa da ranar shahadar Ayatullah Sayyid Murtadha Mutahari.

A jawabin da ya gabatar a wajen ganawar, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi karin haske kan matsayi maras tamka na ma'aikatar ilimi da tarbiyya bugu da kari kan gagarumar rawar da malamai suke takawa wajen tarbiyyar al'umma ma'abota imani, ilimi, dogaro da kai da kuma kyakkyawan fata inda ya ce: Wajibi ne jami'an gwamnati musamman na bangaren tattalin arziki su ba da muhimmanci na musamman ga bangaren ilimi da tarbiyya da kuma batun rayuwar malamai. Su san cewa duk wani kudin da za su kashe a wannan bangaren, wani zuba jari ne saboda gaba da kuma samar da wani yanayi mai girma da kima.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan barazana ta baya-bayan nan da jami'an gwamnatin Amurka suke yi wa Iran a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawar nukiliya tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, Jagoran cewa yayi: Ni dai ba zan amince da tattaunawa karkashin inuwar barazana ba. Wajibi ne jami'an siyasar waje da masu tattaunawar su kula da kuma kiyaye kan iyakokin da aka shata. Haka nan kuma a daidai lokacin da suke ci gaba da tattaunawar, wajibi ne su kiyaye girma da daukakar al'ummar Iran, sannan kuma kada su mika wuya ga duk wata barazana ko wulakanci da tursasawa.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya fara jawabin nasa ne da jinjinawa Ayatullah Shahid Mutahari inda ya bayyana malanta tare da tsarkin niyya da kokari ba kama hannun yaro a matsayin wasu siffofi da Ayatullah Mutaharin ya kebanta da su. Haka nan kuma yayin da yake ishara da rawar da ma'aikatar ilimi da tarbiyya take takawa wajen gina makomar kasa, Jagoran cewa yayi: A fagen ilimi da tarbiyya, ko shakka babu rawar da malamai suke takawa da kuma tasirinsu wajen tsara yanayin tunani da rayuwar dalibai da makomar kasa sun dara irin rawar da iyaye da kuma al'umma suke takawa.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Bisa la'akari da irin wannan matsayi da ma'aikatar ilimi da tarbiyya da kuma malamai suke da shi cikin makomar kasar nan, don haka duk wani kudin da za a kashe a wannan bangaren, a hakikanin gaskiya zuba jari ne.

Haka nan yayin da yake jaddada cewa da irin wannan kallo da mahanga ce ya kamata a tsara dukkanin tsare tsaren ma'aikatar ilimi da tarbiyya, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da irin gagarumar rawar da malamai suke takawa wajen tarbiyyar manyan mutane da suka yi fice inda ya ce: Babban aikin malamai shi ne tarbiyyar zuriya ma'abociyar imani, ilimi, dogaro da kai, kyakkyawan fata ga makoma, ma'abociyar kokari, mahanga mai kyau da kuma cikakkiyar lafiya ta jiki da ruhi.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: A hakikain gaskiya, nauyin da ke wuyan malamai shi ne samar da al'umma madaukakiya a matsayin ci gaba da nauyin da ke wuyan Annabawa, wato koyarwa da kuma tsarkakewa.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar cimma manufa da sakon malamai na hakika wani lamari ne dake da bukatuwa da wasu abubuwa inda ya ce: Daya daga cikin wadannan wajiban shi ne kula da batun rayuwar yau da kullum ta malamai. Wajibi ne jami'an gwamnati, duk kuwa da ‘yan matsalolin da ake fuskanta, su ba da muhimmanci na musamman da ma'aikatar ilimi da tarbiyya da kuma malamai. Su sanya hakan a sahun gaba na ayyukansu.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan cewa idan har aka gafala da batun rayuwar malamai, to kuwa makiya za su iya mummunan amfani da hakan, Jagoran cewa yayi: Tabbas malamai mutane ne ma'abota imani da sanin ya kamata sannan kuma sun fahimci irin makirce makircen makiya da sauran masu bakar aniyar kan gwamnatin Musulunci wadanda suke son amfani da batun rayuwar malamai wajen haifar da fitina da rikici.

Haka nan kuma yayin da yake bayanin cewa yanayin da ake ciki a Iran wani yanayi ne mai kyau wajen haifar da sauye-sauyen da suka dace a fagen ilimi da tarbiyya inda ya ce: Alhamdu lillahi a yau kasar nan tana cikin yanayi mai kyau na tsaro da kwanciyar hankali, sannan kuma jami'an gwamnati sun zage damtse wajen gudanar da ayyukansu. Don haka akwai fage mai kyau na isar da fagen ilimi da tarbiyya zuwa ga yanayi kyau abin bukata.

A karshen jawabinsa kan wannan bangaren, Jagoran ya sake jaddada jinjinawarsa ga malaman da cewa: Daga wannan wajen ina isar da gaisuwa da sallama ta ga dukkanin malaman kasar nan.

A bangare na biyu na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi karin bayani kan mu'amalar wasu jami'an Amurka da al'ummar Iran a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan shirin nukiliyan kasar inda yayi nuni da wasu lamurra.

Jagoran juyin juya halin Musulunci dai ya fara ne da ishara da wani lamari mai muhimmanci inda ya ce: Tsawon shekaru 35 din da suka gabata, makiyan tsarin Musulunci (na Iran), duk kuwa da adawa da gabar da suke yi, amma a koda yaushe sun kasance masu fahimta da kuma lura da daukaka da kuma haibar al'ummar Iran da tsarin Jamhuriyar Musulunci.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Wannan haiba da daukaka, ba na boge ba ne, face dai na hakika ne. Don kuwa kasar Iran mai girma, wacce take da mutanen da suka dara miliyan saba'in, tana da tsohon tarihi da al'adu na asali sannan kuma ga jaruntaka da azama abar misali.

Haka nan kuma yayin da yake jaddada cewar a koda yaushe al'ummar Iran sun kasance masu kare mutumci da matsayinsu, Jagoran cewa yayi: A yayin shekaru takwas na kallafaffen yaki, dukkanin ma'abota karfin duniya sun yi iyakacin kokarinsu wajen dunkufar da wannan al'ummar, amma sun gaza. A saboda haka wajibi ne a kiyaye wannan daukaka da haibar.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Kamar yadda jami'an da dama daga cikin kasashen duniya suke fadi a fili da a boye cewa idan da a ce irin wannan takunkumi da matsin lamba da ake yi wa al'ummar Iran a kan kowace kasa ta daban ne, to da kuwa wannan kasar ta ruguje. Amma Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta ci gaba da tsayuwa da kafafunta.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Lalle wannan ba karamin lamari ba ne. To amma cibiyoyin farfagandar duniya a koda yaushe suna kokarin wajen hana al'ummomin sauran kasashe fahimtar hakikanin abin da ke faruwa a Iran. To amma da dama daga cikin al'ummomin sun san wannan hakikar, kamar yadda jami'an siyasa na duniya sun san hakan, duk kuwa da cewa ba sa fadin hakan a fili, face dai wani abu na daban suke fadi.

Bayan wadannan bayanai, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi jami'an gwamnati musamman jami'an ma'aikatar harkokin waje da kuma masana da masu bakin magana a Iran da cewa: Ku san cewa matukar wata al'umma ta gagara kare matsayi da daukakarta a gaban makiya ‘yan kasashen waje, ko shakka babu za ta sha kashi. A saboda haka wajibi ne a fahimci da kuma girmama daukaka da matsayin da ake da shi.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da barazanar baya-bayan nan da wasu jami'an Amurka suka yi (na amfani da karfin soji a kan Iran) a daidai lokacin da ake ci gaba da tattauna kan makamashin nukiliya, Ayatullah Khamenei cewa yayi: Tattaunawa karkashin inuwar barazana ba ta da wata ma'ana. Al'ummar Iran kuwa ba za ta taba amincewa da tattaunawa karkashin inuwar barazanar ba.

Har ila yau kuma yayin da yake sake ishara da maganganun wasu jami'an Amurkan da suke cewa idan har hakan ta faru to kuwa za su kawo hari wa Iran, Jagoran ya kirayi jami'an gwamnatin Amurkan da cewa: Da farko dai wannan shirme ne kawai. Na biyu kamar yadda a lokacin tsohon shugaban kasar Amurka na fadi cewa a halin yanzu dai an kawo karshen lokacin da za ku kai bugu shi kenan (ta sha kenan). Al'ummar dai ba za ta taba barin wanda yake son wuce gona da iri a kanta ba haka kawai ba.

Har ila yau kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce wajibi ne dukkanin jami'an gwamnati musamman wadanda suke tattaunawar su fahimci wannan lamarin da kuma kiyaye shi, daga nan kuma sai ya ce: Wajibi ne a koda yaushe masu tattaunawa su dinga la'akari da kan iyakokin da aka shata, su yi kokari wajen ganin ba su ketare wadannan kan iyakokin ba.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Lalle wannan ba abu ne da za a taba amincewa da shi ba cewa a daidai lokacin da ake tattaunawa, daya bangaren da ake tattaunawa da shi din ya ci gaba da barazana ba.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Idan har bukatar Amurkawa ga tattaunawar nan ba ta dara ta mu ba, to kuwa ba ta gaza ba. Mu muna fatan ganin tattaunawar nan ta kai ga gaci da kuma dauke takunkumi. To amma hakan ba yana nufin cewa idan ma ba a dauke takunkumin ba, ba za mu iya ci gaba da gudanar da kasar nan ba.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: A halin yanzu dai a cikin gida kowa ya fahimci cewa magance matsalar tattalin arziki na kasar nan bai ta'allaka da dage takunkumi ba. Face dai za a iya magance matsalolin cikin gida ne ta hanyar tsare-tsare masu kyau da kuma irin kwarewar da muke da su, shin an dauke takunkumi ne ko kuma ba a dauke ba.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Na'am mai yiyuwa ne idan da babu takunkumin, da magance matsalolin tattalin arzikin yayi sauki. To idan ma aka ci gaba da takunkumin, za a iya magance matsalolin.

Haka nan kuma yayin da yake kara tabbatar da cewa wannan dai ita ce matsayar Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan batun tattaunawar nukiliya da ake yi, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi karin bayani kan gagarumar bukatar da Amurka take da ita ga wannan tattaunawar inda ya ce: Don su sami wani abin da za su nuna a matsayin nasarar da suka samu, don haka suna da bukatar wata damar da za su ce "mun tilasta wa Iran zama teburin tattaunawa da kuma tilasta mata wasu abubuwa".

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: Ni dai ba zan amince da tattaunawar da za a gudanar da ita karkashin inuwar barazana ba". Don haka ne ma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi tawagar Iran a wajen tattaunawar da cewa: Ku ci gaba da tattaunawar ta hanyar kiyaye kan iyakokin da aka shata. Babu matsala idan har kuka cimma wata matsaya. To amma koda wasa kada ku taba mika wuya ga duk wani tilasci, nuna karfi, kaskanci da kuma barazana.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewa a halin yanzu dai Amurka ita ce gwamnatin da aka fi kyama a duniya sakamakon ayyuka da siyasarta wanda daya daga cikin irin wadannan ayyuka shi ne goyon baya a fili da take ba wa gwamnatin Saudiyya a hare-haren wuce gona da irin da take kai wa al'ummar Yemen. Jagoran ya ce: Gwamnatin Al Sa'ud, ba tare da wani dalili ba face dai cewa da wani dalili ne mutanen Yemen za su ce ba sa son wane a matsayin shugaban kasa, suke ci gaba da kashe mata da kananan yaran da ba su ci ba su sha ba a kasar, ita kuma Amurka tana ci gaba da goyon bayan wannan gagarumin danyen aiki.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Amurkawa ba tare da kunya ba suna ci gaba da goyon bayan kisan gillan da ake yi wa al'ummar Yemen, amma kuma a bangare guda suna tuhumar Iran wacce take kokarin aikewa da taimakon agaji da suka hada da abinci da magunguna ga al'ummar Yemen, da tsoma baki cikin lamurran cikin gidan Yemen da aikewa da makamai.

Ayatullah Khamenei ya ci kara da cewa: Al'ummar kasar Yemen ma'abota gwagwarmaya da tsayin daka ba sa bukatar makamai, don kuwa dukkanin cibiyoyin soji da barikokinsu suna hannunsu ne. Suna bukatar agaji na gaggawa ne sakamakon killacewa da takunkumin abinci da magunguna da makamashi da kuka sa musu ne. To amma hatta shigowar kungiyar agaji ta Red Crescent (don taimaka musu) kun hana.

Daga karshe dai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewar tafarkin da al'ummar Iran suka zaba, tafarki ne mai karfi sannan kuma mai kyakkyawar makoma. Don haka sai ya ce: Da yardar Allah sannan kuma koda makiya ba sa so, wannan tafarki zai yi nasara, sannan kuma kowa zai ga cewa makiya ba za su iya aiwatar da bakar aniyarsu a kan al'ummar Iran ba.

3260702

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: