IQNA

An Kammala Gasar Hardar Kur’ani Mai Tsarki Da Tajwidi Ta Duniya A Kasar Tunisia

23:08 - May 08, 2015
Lambar Labari: 3274326
Bangaren kasa da kasa, an kamala gasar hardar kur’ani mai tsarki da tajwidi ta kasa da kasa a bababn masallacin Zaitunah da ke birnin Tunisia na kasar Tunisia tare da bayar da kyautuka ga wadanda suka nuna kwazo daga na daya zuwa na biyar.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alfajr cewa, a jiya an gudanar da taron kamala gasar hardar kur’ani mai tsarki da tajwidi ta kasa da kasa a bababn masallacin Zaitunah da ke birnin Tunisia na kasar Tunisia tare da bayar da kyautuka ga wadanda suka nuna kwazo daga na daya zuwa na biyar a dukkanin bangarorin gasar.

 

Bayanin ya ci gaba da cewa a bangaren hardar dukkanin kur’ani wadanda suka zo na daya  daga kasar Tunisia sun hada Yahya Bin Adel Bin Ali, Anwar Bin Muhammad Bin Ali Bin salamah, Abdlrahmad ahmad Abdallah daga Kuwait, Muhammad Ali Islami daga Iran, Ahmad Ali Ahmad taha daga kasar Lebanon, su ne suka zo na daya zuwa na biyar.

A bangaren Tajwidi da kyawun sauti kuwa Ali Bin saliha daga Tunisia, Ahmad Muhammad ahmad Khalidi daga Morocco, Muhamad Mansur daga Turkiya, Muhamamd Ahmad Zahed daga Lebanon, Reza Golshahi daga Iran, su ne suka zo mataki na daya zuwa na biyar.

 

Gasar dai ta samu halaratr kasashe 32 mahardata 22 sun kara a bangaren hardar dukaknin kur’ani, sai kuma 9 sun kara a bangaren tajwidi da kuma kyautata sautin karatu.

Haka nan kuma gasar ta samu halaratr manyan jami’ai daga ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar, da kuma malamai gami da manyan jami’an gwamnati da suka hada fira ministan kasar.
Hojjatol Eslam Haj Muhammad Abuqasem ya kasance daya daga cikin alkalan da suka yi hukunci a gasar ta karshe.

 

3272218

Abubuwan Da Ya Shafa: tunis
captcha