IQNA

Makircin Masu Kyamar Musulunci A Jamus Tamkar Zane Ne Kan ruwa

21:45 - May 09, 2015
Lambar Labari: 3277830
Bangaren kasa da kasa, jami’an ‘yan sanda a kasar Jamus sun sanar da kame gungun wasu mutane da ke shirin kai hare-hare kan masallatai da otel na musulmi a kasar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gzioa na kasar Faransa cewa, kotun kasar Jamus ta ce an samu wasu abubuwa masu tsananin tarwatsewa tare da mutanen da aka kame masu kyamar muslunci.



Shugaban musulmin kasar Jamus ya bayyana cewa hare hare a kan masallatayya da kuma musulmi a kasar yana dada karuwa a kasar, ya kara da cewa yana fadar haka a ranar Asabar da ta gabata a shafinsa na labaria na yanar gizo, inda ya kara da cewa, hare haren sun fi shafar mata musulmi masu sanya  hijabi ko kuma dankwali .



Mazyek ya kara da cewa a duk mako suna samun rabarain cewa an kaiwa wani masallaci, ko cibiyar addinin Musulunci ko kuma  an walakanta limamin wani masallaci ko kuma an kaiwa wata musulma sanye da hari a kasar.

Shugaban musulman na kasar Jamus yace  yana zargin kungiyar  nan da ake kira pegida wacce kuma ta daukawa kanta yaki da yaduwar addinin Musulunci a kasashen Turai.



Kungiyar  ta sha gudanar da zanga zangar  mako mako a cikin watannin da suka gabata a  birnin dresden na gabacin kasar Jamus, inda kuma ta samu magoya baya kimani dubu ashirin da biyar a cikin dan watannin da suka gabata.



3275751

Abubuwan Da Ya Shafa: jamus
captcha