IQNA

Murkushe Al’ummar Bahrain Da Karfin Tuwo Ba Zai Taba Karya Musu Gwiwa ba

21:47 - May 09, 2015
Lambar Labari: 3277831
Bangaren kasa da kasa, Sheikh Khalid Fadil Zaki limamin masallacin Imam sadeq (AS) a yankin Deraz na kasar Bahrain ya bayyana cewa murkushe zanga-zangar al’ummar da karfin tuwo ba zai raunana su ba.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almanar cewa, a jiya a lokacin sallar juma’a Sheikh Khalid Fadil Zaki limamin masallacin Imam sadeq (AS) a yankin Deraz na kasar Bahrain ya bayyana cewa murkushe gangamin al’umma na lumana da karfin bindiga da mahukuntan kasar ke, ba zai taba sanbya al’umma ta yi rauni wajen neman hakkinta ba ko alama.

 

Shi ma a nasa bangaren babban malamin Addinin Musulunci na Kasar ta Bahrain ya ce; Kokarin da gwamnatin kasar ke yi na murkushe masu zanga-zangar lumana zai ci tura, Shehin Malamin yana cewa; Murkushe Zanga-zangar ‘yan hamayyar kasar da mahuknta ke yi domin tilasta su mika wuya ga masu mulki, wani lamari ne da zai ci tura.

Da ya ke yin ishara da yadda jami’an tsaron kasar su ke amfani da karfi akan masu Zanga-zangar lumana ta neman kawo sauyi ya ce; babu abinda zai karawa mutane idan ba karfin azama da hadin kai ba, Kusan mako guda kenan da al’ummar kasar ta Bahrain su ke Zanga-zangar neman sakin daya daga cikin jagororin ‘yan hamayya da aka kama.

 

Malamin ya kara da cewa duk da irin matakan rashin Imani da mahukuntan kasar ta Bahrain suke dauka kan al’umma da nufin murkushe su da karfin bindiga da kuma kamu gami da azabtarwa, amma duk da hakan al’umma ba ta yi rauni ba, kuma hakan shi ne zai sama sanadiyyar samun canjin da suke ji ma tsoro.

Gwamnatin Bahrain dai ta jima tana dsauklar dukkanin matakai na yin amfani da karfi da daukar haya daga kasashen ketare domin murshe al;ummar kasar, amma duk da hakan bas u ja da baya ko nuna gazawa ko tsoron rashin imanin da mahukuntan ke nunawa ba.

 

3274470

Abubuwan Da Ya Shafa: bahrain
captcha