Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Anatoli cewa, Tasnim Ahmad Sheikh ‘yar majalisar dokokin kasar Birtaniya daga yankin Scotland ita ce mace ta farko musulma da ta lashe zaben majalisar dokokin kasar ta Birtaniya daga wannan yanki.
Ta ce wannan wata babbar dama ce ta samu wadda za ta yi al’ummarta aiki, kuma za ta kare hakkokin muuslmi mata musamman da ake muzgunawa saboda su ne marassa rinjaye, tare da shan alawashin aiwatar da alkawalunn da ta dauka a lokacin yakin neman zabe.
Matar yar shekaru 44 da haihuwa tana raya 4 da ta haifa kuma ita mamba cea jam’iyyar yan kasa ta yankin Scotland da ta tsaya takara a wannan karo kuma ta samu nasara duk kuwa da cewa ita musulma ce.
Daga cikin yan majalisar dokokin kasar Biratniya musulmi 13 da suka samu nasarar lashe zaben 8 daga cikinsu dai mata ne, wanda kuma wannan shi ne karo na farko da aka samu hakan.
A cikin shekara ta 2010 wadda ita ce musulmi suka fi samu kujeru a majalisar dokokin kasar ta Birtaniya, dukkaninsu dais u 8 ne suka je majalisar a lokacin.
3297551