Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya an fitar da wani littafi bisa kokarin malamai da ke bayani kan rayuwar Imam Musa Kazim (AS) dangane rayuwarsa a dukkanin bangarori da kuma irin gdunmawar da ya bayar a fagen habbaka addinin muslunci kamar yadda kakanninsa (AS) suka yi a tarihinsu mai tsarki.
A daya bangaren kuma dubban daruruwan mutane ne ke ci gaba da isa birnin Kazimiyya na kasar Iraki, domin halartar tarukan tunawa da zagayowar ranar shahadar Imam Musa Kazim (AS).
Rahotanni daga kasar sun yi nuni da cewa tun kwanaki biyu da suka gabata ne dubban daruruwan Irakawa daga sassa daban-daban na kasar suke ta isa birnin Kazimiyya a hubbarensa (AS mai tsarki, domin halartar tarukan zagayowar ranar shahadar tasa Imam Musa Kazim (AS), daya daga cikin limaman iyalan manzon Allah.
Wanda za a gudanar a hubbarensa Imam Kazim (AS) da ke birnin na Imam kazim (AS), a bangare guda kuma dubban jami'an tsaron kasar Iraki a cikin kayan sarki sun dauki kwararn matakan tsaro a cikin birnin na Imam Kazim (AS) da ma kan hanyoyin da ke isa birnin, domin bayar da kariya ga masu halartar taruka daga hare-haren ta'addanci.
3298617