IQNA

Aiwatar Da Siyasar Masu Girmai Kai Da Yi Musu Yaki A Yankin / Dawo Da Jahiliyyar Kafin Musulunci

23:43 - May 17, 2015
Lambar Labari: 3304636
Bangaren siyasa, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei a ganawarsa da jami’an gwamnati da kuma jakadojin kasashen ketare ya bayyana hadarin da yanking abas ta tsakiya ke fsukanta ta hanyar aiwatar da bakar siyasar kasashen ketare da wasu ke yi.


Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jagora cewa, a safiyar Asabar wacce ta yi daidai da zagayowar ranar da aka aiko Ma'aiki (s.a.w.a) a matsayin Manzo, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da manyan jami'an kasar Iran, jakadun kasashen musulmi bugu da kari kan wasu gungun mutanen da suka fito daga bangarori daban-daban na kasar Iran don tunawa da wannan rana mai girman matsayi.

A jawabin da ya gabatar wajen taron, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da wajibcin amfanuwa da kuma riko da darussan da suke cikin aiko Ma'aiki (s.a.w.a) wajen fada da sabuwar jahiliyya ta wannan lokacin wacce ta fi hatsari da sarkakiya sama da jahiliyar gabanin Musulunci, wanda ya ce ma'abota girman kan duniya karkashin jagorancin Amurka su ne ummul aba'isin din kafuwar wannan sabuwar jahiliyar. Daga nan sai ya ce: Tarihin shekaru 35 da suka gabata na Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya tabbatar da cewa al'umma tana iya tsayawa kyam wajen tinkarar wannan jahiliyar sannan kuma ta yi nasara a kan ta matukar ta kiyaye abubuwa biyu, wato ‘basira' ‘azama da himma'.

Haka nan kuma yayin da yake taya al'ummar Iran da sauran al'ummar musulmi na duniya da dukkanin ‘yantattu na duniya murnar zagayowar wannan rana ta aiko Ma'aiki (s.a.w.a), Jagoran ya bayyana cewa bil'adama suna da bukatar darussan da suke cikin aiko Ma'aiki (s.a.w.a), daga nan sai ya ce: An aiko Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa, don fada da jahiliya ba wai kawai jahiliyar Jazirar larabawa, face har ma da sauran ‘yan mulkin mallaka na wancan zamanin.

Ayatullah Khamenei ya bayyana ‘sha'awa' da kuma ‘fushi' a matsayin wasu siffofi na asali na wancan jahiliyar, daga nan sai ya ce: A wancan zamanin Musulunci yayi fada ne da irin batar da aka sanya bil'adama a ciki wadanda a wani bangaren sun samo asali ne daga sha'awa ta son zuciya da sha'awa ta jima'i, a daya bangaren kuma daga fushi da tsananin rashin imani da tausayi.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da sake dawo da irin wancan jahiliyar ta gabannin Musulunci a wannan zamani na mu ita din ma karkashin inuwar wadannan ababe guda biyu na ‘sha'awa' da ‘fushi da rashin tausayi', Jagoran cewa yayi: A halin yanzu ma dai muna ganin bayyanar irin wannan sha'awar ta rashin hankali da kuma zalunci da rashin tausayi da zubar da jini maras iyaka, bambancin kawai shi ne cewa abin bakin cikin jahiliyar ta yanzu tana rike ne da makami na ilimi da masaniya, wanda hakan ya fi hatsari.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Ko da yake a daya bangaren shi ma Musulunci yayi amfani da irin karfin da yake da shi wajen yaduwa a duniya, sannan kuma akwai gagarumin fatan samun nasara, amma da sharadin an yi amfani da ‘basira' da ‘azama da kuma himma'.

Ayatullah Khamenei ya bayyana halin da duniyar musulmi take ciki a halin yanzu na rashin tsaro, kisan juna da kuma kame wasu yankuna na kasashen musulmi da ‘yan ta'adda suka yi a matsayin daya daga cikin misalan sabuwar jahiliya ta wannan zamanin da ma'abota girman kan duniya karkashin jagorancin Amurka suka tsara. Daga nan sai ya ce: Don cimma wannan bakar aniya ta su da kuma kare haramtattun manufofinsu, wadannan mutanen suna amfani da kafafen farfaganda da yada karya. Daya daga cikin misalan hakan kuwa shi ne ikirarin Amurka na fada da ta'addanci.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Amurkawa suna wannan ikirarin ne a daidai lokacin da su da kansu suke fadin cewa suna da hannu wajen samar da mafi hatsarin kungiyoyin ‘yan ta'adda irin su kungiyar Da'esh (ISIS). Amurka a hukumance take goyon bayan kungiyoyin ‘yan ta'adda. Haka nan kuma Amurka a fili take goyon bayan haramtacciyar gwamnatin sahyoniyawa wacce ta mamaye da kuma ci gaba da zaluntar Palastinawa a Gaza da Yammacin Kogin Jordan. Amma a baki suna ikirarin fada da ta'addanci. To wannan dai ita ce wannan sabuwar jahiliyyar.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi dukkanin kasashen musulmi da cewa: Ya kamata al'ummar Iran, al'ummar musulmi na duniya da kuma shugabannin kasashen musulmi su san cewa lalle za mu iya tsayin daka a gaban wannan jahiliyar.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar tushen bakar siyasar ma'abota girman kan duniya a a yankin Gabas ta tsakiya sannan kuma a irin wannan yanayi da ake ciki, ita ce haifar da yaki na wakilci inda yace: A halin yanzu babban abin da wadannan mutane suka sa a gaba shi ne kare manufofinsu da jika aljihunan kamfanonin kera makamansu. A saboda haka wajibi ne kasashen yankin nan su yi taka tsantsan, don kada su fada tarkon wannan siyasar.

Jagoran ya bayyana ikirarin kare tsaron yankin Tekun Fasha a matsayin wani ikirari na karya da Amurkawan suke yi, daga nan sai ya ce: Tsaron Tekun Fasha lamari ne da ke wuyan kasashen yankin wadanda suka yi tarayya cikin manufofi, ba wai Amurka ba. A saboda kasashen yankin Tekun Fasha su ne za su kare tsaro da zaman lafiyan yankin.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce Amurka dai ba tana son tabbatar da tsaron yankin Tekun Fasha ba ne, don haka ba ta da hakkin fadin wani abu kan wannan lamarin. Jagoran ya ci gaba da cewa: Matukar aka tabbatar da tsaron yankin Tekun Fasha, to dukkanin kasashen yankin ne za su amfana da haka. To amma matukar aka ratsa tsaron, to kuwa dukkanin kasashen yankin ne za su cutu da kuma zama cikin rashin tsaro.

Wani misali na rashin gaskiyar ikirarin Amurka na tabbatar da tsaro da zaman lafiyan yankin nan da Ayatullah Khamenei ya kawo shi ne abin da ke faruwa a kasar Yemen inda ya ce: A halin yanzu dai an mai da kasar Yemen ta zamanto wani fage na zubar da jinin kananan yara da matan da ba su ci ba su sha ba, wanda a zahiri masu aikata hakan musulmi ne, to amma wadanda suka tsara hakan kana kuma ummul aba'isin dinsa ita ce Amurka.

Har ila yau kuma yayin da yake magana dangane da wani ikirarin karyar na Amurka na cewa Iran tana goyon bayan ta'addanci, Ayatullah Khamenei ya ce: Al'ummar Iran dai sun yi fada da dukkanin karfinsu da ta'addancin da aka shigo da shi cikin gidan Iran ta hanyar taimako da kudaden Amurka, to amma kuma suna zargin Iran da goyon bayan ta'addanci. Alhali kuwa Amurka ce a fili take goyon bayan ta'addanci.

Haka nan kuma yayin da yake bayyana cewar al'ummar Iran sun kasance kuma a nan gaba ma za su ci gaba da kasancewa masu fada da ta'addanci, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: Al'ummar Iran dai za ta ci gaba da goyon bayan al'ummomin kasashen Iraki, Siriya, Labanon da Palastinu da aka mamaye wadanda suka tsaya kyam wajen fada da da ‘yan ta'adda da kuma sahyoniyawa ‘yan ta'adda.

Har ila yau kuma yayin da yake magana kan wasu ayyukan ta'addanci da gwamnatin Amurka take aikatawa, Ayatullah Khamenei ya kirayi ‘yan siyasar Amurkan da cewa: Ku din nan, ku ne ‘yan ta'adda. Ta'addanci aikinku ne. Mu dai muna adawa da ta'addanci, za mu ci gaba da fada da hakan da kuma goyon bayan duk wani da ake zalunta.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana al'ummomin kasashen Yemen, Bahrain da Palastinu a matsayin al'ummomin da ake zalunta inda yace: A daidai lokacin da a farkon Musulunci, mushirikan Makka su kan dakatar da yaki a watannin da aka haramta yaki. Amma a yau a kasar Yemen, a cikin watan Rajab wanda daya ne daga cikin watannin harami (da yaki ya haramta a cikinsu), ana ci gaba da ruwan bama-bamai da makamai masu linzami a kan al'ummomin wannan kasar da ba su ci ba su sha ba.

Haka nan kuma yayin da yake bayanin cewa goyon baya da kuma ba da kariya ga wanda ake zalunta wani umurni ne na Musulunci, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: Mu dai gwargwadon yadda za mu iya za mu ci gaba da goyon bayan wadanda ake zalunta da kuma fada da azzalumai.

Ayatullah Khamenei ya kirayi kasashen yankin Gabas ta tsakiya da su taka tsantsan dangane da siyasar ma'abota girman kan duniya na samar da wani makiyi na boge da nufin haifar da rikici da yaki a tsakaninsu inda ya ce: Dukkanin kokarinsu shi ne boye makiya na asali wadanda su ne ma'abota girman kan da ‘yan amshin shatansu da kuma sahyoniyawa, sannan kuma su hada kasashen musulmi fada da junansu. A saboda haka wajibi ne a yi fada da wannan siyasa ta sabuwar jahiliya.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Shekaru aru aru kenan ma'abota girman kan duniya suke ta kokari wajen ganin bayan irin farkawa ta Musulunci da kuma gwagwarmaya da zalunci da ta kunno kai a wannan yankin. Haka nan kuma tsawon shekaru 35 din da suka gabata babu irin kokarin da ba su ba wajen fada da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayinta na tushen irin wannan farkawa ta Musuluncin. To amma a kullum sun sha kashi, a nan gaba ma za su ci gaba da shan kashin.

Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musuluncin, sai da shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya gabatar da jawabinsa inda ya taya al'ummar musulmi murnar wannan rana mai albarka inda ya kirayi al'ummar musulmi da su yi riko da koyarwar da Annabi (s.a.w.a) ya zo da su a matsayin abin da zai samar musu da tsira duniya da lahira.

Har ila yau kuma shugaban na Iran ya sake jaddada mahangar al'ummar Iran na ci gaba da kare hakkokinsu da kuma neman sulhu da zaman lafiya, sai dai yace duk wani da yayi kokarin wuce gona da iri kan al'ummar Iran, to kuwa zai fuskantar gagarumin mai da martani daga wajen al'ummar na Iran.

3304067

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha