IQNA

Ba Za Mu Bari A Duba Cibiyoyinmu Na Soji Ba / Jawabi Ne Ga Manyan Shaidanun Duniya

23:56 - May 21, 2015
Lambar Labari: 3306227
Bangaren siyasa, jagoran juyin jya halin muslunci ya bayyana cewa ko alama ba za su taba bari a duba ko daya daga cikin cibiyoyinsu na soji ba a kan batun tattaunawar da ke gudana kan batun nukiliya.


Kamfanin dilalncin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jagora cewa, a safiyar Laraba 20-05-2015 ce, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya halarci bikin yaye daliban jami'ar jami'an dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran da aka gudanar a jami'ar soji ta Imam Husaini (a.s) don tunawa da ranar dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran da kuma ranar 3 ga watan Khordad, ranar da dakarun Iran din suka kaddamar da hare-haren Baitul Mukaddas da ‘yanto garin Khoramshahr a lokacin kallafaffen yaki.

Jim kadan bayan isowarsa wajen bikin, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya fara da halartar makabartar shahidan jami'an inda yayi musu addu'ar neman karin matsayi a wajen Allah. Daga nan kuma sai Jagoran wanda kuma shi ne babban kwamandan dakarun kasar Iran ya duba faretin dakarun da suke filin taron.

A jawabin da ya gabatar a wajen bikin, Ayatullah Khamenei ya bayyana ‘mahangar Musulunci' da ‘mahangar jahiliyya' a matsayin wasu mahanga na asali guda biyu da suke yawo a duniyarmu ta yanzu wadanda babu yadda za su iya tafiya tare da juna. Haka nan kuma yayin da yake ishara da sabbin maganganun da wasu daga cikin kasashen da Iran take tattaunawa da su kan shirin nukiliyanta da suka hada da bukatar kai ziyara da sanya ido kan cibiyoyin sojin kasar da kuma tattaunawa da masanan kasar da suke gudanar da ayyukansu a fagen nukiliyan, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Ko da wasa ba za a taba ba da wannan izinin ba. Sannan kuma ya kamata makiya su san cewa al'umma da jami'an kasar Iran ba za su taba yin kasa a gwiwa wajen tinkarar duk wani wuce gona da iri da kokarin nuna karfi a kansu ba.

Har ila yau kuma yayin da yake ishara da labarin da ke nuni da kokarin da makiyan al'ummar Iran bisa hadin gwiwan jami'an wasu kasashen larabawan Tekun Fasha na haifar da yaki a kan iyakokin kasar Iran, babban kwamandan dakarun kasar ta Iran cewa yayi: Matukar gigi ya debe su suka yi wani shaidanci, to kuwa Iran za ta mayar musu da martani mai kaushin gaske.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan dakarun kare juyin juya halin Musulunci da kuma irin nasarorin da suka samu a fagen tunani da kuma aiki, Ayatullah Khamenei cewa yayi: Wannan jami'a ta Imam Husaini (a.s), daya ce daga cikin alamomin da suke nuni da kamala da kuma ci gaban dakarun kare juyin juya halin Musuluncin.

Haka nan kuma yayin da yake magana da daliban jami'ar ta Imam Husaini (a.s), Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa yayi: A yau tutar yunkurin juyin juya halin Musulunci da kuma tutar sabuwar mahanga ta Musulunci ta iso ga hannunku ne. Don haka wajibi ku ma ki rike ta da kyau kamar yadda wadanda suka gabace ku suka rike.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana mahangar Musulunci a matsayin wata hanyar tabbatar da sa'adar bil'adama da kuma zuriya masu zuwa inda ya ce: Marigayi Imaminmu mai girma ne ya jagoranci samar da wannan yunkuri abin alfahari, sannan kuma al'ummar Iran suka daga wannan tutar sakamakon sadaukarwarsu.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da wata mahangar da ta yi hannun riga da ta Musulunci wacce ita ce mahangar jahiliyya, Ayatullah Khamenei cewa yayi: A yau dai wannan mahanga ta jahiliyya, wacce mahanga ce ta zalunci, tinkaho da karfi, girman kai da son kai da ma'abota girman kan duniya suke wa jagoranci, tana fada ne da mahanga da koyarwar Musulunci wacce take goyon bayan tabbatar da adalci, ‘yancin bil'adama da kuma kawar da fagen jari hujja da mulkin mallaka.

Har ila yau kuma yayin da yake magana kan cewa idanuwan da dama daga cikin al'ummomin ba za su iya gano wadannan mahangar ba da kuma fahimtar yunkurin da ke cike da munafunci na ma'abota sabuwar jahiliyyar karkashin inuwar wasu kalmomi masu dadin ji irin su kare hakkokin bil'adama da nesan rikici da amfani da karfi, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: Babu yadda za a yi wadannan mahanga guda biyu su tafi tare da junansu. Don kuwa daya mahangar ta ginu ne bisa tushen zalunci da kiyayya da al'ummomi alhali daya mahangar kuwa tana magana ne kan goyon bayan wadanda ake zalunta da kuma fada da azzalumai.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan farfagandar da makiya suke yadawa na cewa a halin yanzu an mai da Iran ta zama saniyar ware, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa yayi: Tun farko har zuwa yanzu Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da matsayi a zukatan al'ummomin duniya, babbar abin da ke tabbatar da hakan shi ne irin so da kaunar da al'ummomin duniya suke nuna wa shugabannin Jamhuriyar Musulunci ta Iran tsawon shekaru talatin da shidan da suka gabata.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar sunan al'ummar Iran a wajen al'ummomi kai hatta tsakanin ‘yan siyasan kasashen duniya ma'abota ‘yancin kai, wani suna ne mai girman matsayi inda ya ce: Mutumin da aka mayar da shi saniyar ware, shi ne wanda ta hanyar amfani da karfi da kuma dukiya (dala) ce zai iya janyo hankulan wasu mutane.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da cewa al'ummar Iran sun sami daukakar da suke da ita ne albarkacin Musulunci da kuma wannan yunkuri na su da ke cike da ‘yanci, Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayi ishara da wasu kalubalen da suke fuskantar gwamnatin Musulunci ta Iran din inda ya ce: Lalle mu dai ba ma cikin wata damuwa saboda bayyanar wadannan kalubalen, don kuwa kasantuwar kalulbale wata alama ce da take nuni da samuwar wani yunkuri da kuma ci gaban da ake samu.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Lalle al'ummar Iran za ta tsallake wadannan kalubalen ta hanyar dogaro da Allah da kuma dogaro da kanta.

Ayatullah Khamenei ya bayyana son amfani da karfi da neman wuce gona da irin ma'abota girman kai cikin tattaunawar nukiliya da ke gudana tsakanin Iran da manyan kasashen duniya a matsayin daya daga cikin wadannan kalubalen da ake fuskanta inda ya ce: Har ya zuwa yanzu makiya ba su fahimci al'umma da jami'an gwamnatin Iran ba don haka suke fadin irin wadannan maganganu na tinkaho da karfi. Don kuwa har abada al'ummar Iran da kuma gwamnatinsu ba za su taba mika kai ga maganganun nuna karfi ba.

Jagoran ya bayyana cewar gwargwadon yadda aka mika wuya ga ma'abota girman kan gwargwadon yadda za su ci gaba da kokarin nuna karfin don haka sai ya ce: Wajibi a gina wata karfaffiyar katanga ta azama da dogaro da Allah da kuma jingina da karfi na kasa a gaban irin wannan kokarin nuna karfi.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana abin da wasu daga cikin kasashen da Iran take tattaunawa da su kan shirin nukiliyan na cewa wajibi ne Iran ta bari a dinga gudanar da bincike a cibiyoyinta na soji da kuma tattaunawa da masanan Iran da suke gudanar da ayyukansu a fagen nukiliyan a matsayin wata alama ta kokarin wuce gona da irin da tinkaho da karfi na ma'abota girman kan suke nunawa. Daga nan sai ya ce: kamar yadda na fadi a baya, ba zan taba barin a gudanar da bincike a wata cibiya daga cikin cibiyoyin soji, haka nan da kuma tattaunawa da masanan nukiliya da sauran fannoni masu muhimmanci ba ko kuma cin zarafinsu ba.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Ba zan taba bari ‘yan kasashen waje su zo su yi magana da masana da ‘ya'yan wannan al'umma masu girma da kuma yi musu tambayoyi ba.

Jagoran ya ce babu wata al'umma ko kuma gwamnati mai hankali da za ta amince da wannan aikin. Daga nan sai ya ce: Wawayen makiyanmu, suna tunanin cewa za mu bari su zo su yi tambayoyi ga masana da masu bincikenmu kan wani ci gaba da suka samu. Ko shakka ba za a taba barin hakan ta faru ba. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Lalle ya kamata makiyan gwamnatin Musulunci ta Iran da kuma dukkanin wadanda suke fatan ganin hakan ta faru su fahimci wannan lamarin da kyau.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Ya kamata jami'an gwamnatinmu masu girma, wadanda suke ci gaba da tafiya a kan wannan tafarkin cikin jaruntaka, su san cewa hanya guda ta tinkarar wadannan wawayen makiyan, ita ce tsayin daka da rashin mika kai. Jagoran ya kara da cewa: Wajibi ne jami'ai da kuma tawagar masu tattaunawar su bayyanar da daukakar al'ummar Iran.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce dukkanin jami'an gwamnatin ta Iran sun sami wannan matsayi ne albarkacin wannan juyi na Musulunci don haka sai ya ce: Dukkaninmu masu hidima wa al'umma ne, don haka akwai nauyi a wuyanmu na mu tsaya kyam a gaban masu tinkaho da karfi da kuma makirce makircensu.

A ci gaba da jawabin nasa, Ayatullah Khamenei yayi ishara da wasu labarurruka da suke nuni da kokarin makiya da wasu wawayen jami'an wasu kasashen yankin Tekun Fasha na kokarin haifar da yaki a kan iyakokin Iran da nufin biyan bukatun ma'abota girman kan duniya inda ya ce: Wajibi ne dukkanin dakarun kare juyin juya halin Musulunci da kuma dukkanin masu kare hurumi da tabbatar da tsaron kasar Iran su zamanto cikin shiri, ta yadda idan har suka yi wani shaidanci, to kuwa za su fuskanci gagarumin mai da martani daga wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan cewa al'ummar Iran za ta ci gaba da tafiya bisa tafarkin da ta zaba wa kanta, Jagoran cewa yayi: Ko shakka babu ci gaba da riko da wannan tafarkin yana tattare da wahalhalu. Don kuwa tsawon tarihi al'ummomin da suka sami kambun zinare a bisa tafarkin da suke kai sun sami hakan sakamakon rashin rusunawa kalubalen da suka kunno musu kai, sannan kuma suka yi tsayin daka wajen tinkarar duk wani wuce gona da iri.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana al'ummar Iran a matsayin alama ta irin wannan al'umma don haka daga karshe yayi fatan cewa matasa da kuma sabbin zuriyar al'ummar Iran za su dau wannan nauyi da suka karba daga wajen al'ummomin da suka gabata da kuma kiyaye shi yadda ya kamata.

Shi ma a nasa jawabin babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran Manjo Janar Muhammad Ali Ja'afari ya bayyana cewar manufar irin shiri da kuma karfin da dakarun kare juyin juya halin Musulunci suke yi a kullum ita ce ba da kariya ga juyin juya halin Musulunci da kuma irin nasarorin da aka samu.

Manjo Ja'afari ya kara da cewa: Dakarun kare juyin juya halin Musulunci, ta hanyar fahimtar irin yanayin da ake ciki da kuma ja-in-ja da ke gudana tsakanin sansanin raunanan duniya da kuma ma'abota girman kai, don haka suna kokari wajen karfafa kansu a dukkan bangarori.

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran din ya ce a halin yanzu dai makiyan al'ummar Iran ba abin da suka sani in ban da karfi na makami don haka ya bayyana cewar dakarun kare juyin juya halin Musulunci a shirye suke su yi magana da su da irin harshen da suke fahimta na amfani da karfi da kuma makamin. Manjo Ja'afari ya ce: Makaman dakarun kare juyin juya halin Musuluncin dai makamai ne na neman tabbatar da adalci da kuma fada da zalunci.

Shi ma a nasa bangaren shugaban jami'ar Imam Husain (a.s) din Admiral Murtadha Safari ya gabatar da rahoto kan ayyukan jami'ar tasa.

Daga karshe dai Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya mika lambobin girma ga dalibai da malaman da suka nuna bajinta, kana daga karshe kuma daliban jami'an suka gudanar da faretin ban girma.

3305835

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha