IQNA

23:47 - May 26, 2015
Lambar Labari: 3308175
Bangaren kasa da kasa, Sayyid Ibarahim Amin sayyid ya bayyan acewa yan takfiriyyah babban hadari ne ga dukkanin musulmi da kiristocin Lebanon da ma daukacin dukkanin mabiya addinai a yankin baki daya.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na skabnews.com cewa, Sayyid Ibarahim Amin sayyid shugaban kwamitin siyasa na kungiyar Hizbulah, ya bayyana cewa, gwagwarmayarsu da yahudawan Sahyuniya ta zo ne domin dakawa hadarin sahyuniyawa burki kan al’ummar kasarsu, amma kuma  ahalin yanzu akidar yan takfiriyyah babban hadari ce ga dukkanin musulmi da kiristocin Lebanon da ma daukacin dukkanin mabiya addinai na sama a yankin gabas ta tsakiya.

Ya ci gaba da cewa ko shakka babu gwagwarmayar kasarsa ta yi imanin cewa yan takfiriyyah yahudawan sahyuniya ne suka samar da su domin cimma burinsu ta hanya mafi sauki, kuma abin takaicxi shi ne yadda ya zama wasu daga cikin kasashen larabawan yankin ne ma aka baiwa kwangilar aiwatar da wannan shin a rusa al’ummar musulmi da kasashen larabawa.

Sayyid Ibrahim ya ci da cewa yan ta’addan takfiriyyah ba su raga wa kowa, domin kuwa an gina su kan akida ta kafirta dk wad ab a cikinsu yake ba, ko da kuwa akidarsu guda, da nufin yin amfani da wannan damar wajen cutar da kowane bangare na musulmi, balantan mabiya addinin kirista d sauran wadanda ba musulmi ba.

Y ace ya zama wajibi a kan dukkanin mabiya addinai musulmi da wadanda ba musulmi su san cewa wajibi ne akansu su yaki akidar takfiriiya tn daga tushe, ta hanyar taka wa kasashehn da suke daukar nauyin wannan mummuna akidar da sunan suna goyon bayan sunna suna cutar da al’ummar musulmi da sauran al’ummomi.

3308064

Abubuwan Da Ya Shafa: Lebanon
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: