Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habartra cewa, wannan gasa dai za a gudanar da ita a matakai wadda dukkanin mahalarta 3000 da ke ciki za su shiga.
A taron bude gasar, Wuld Bu Asriyah babban daraktan ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar ya gabatar da jawabi, tare da Muhammad Mahmud Wuld, da kuma Wasilku Wuld Muhammadu.
Wuld Bu Asriyyah ya bayyana cewa kasar tana bayar da muhimmanci matuka ga batun addinin muslunci baki daya, kama da batun ilmomin addinin muslunci ta bangaren sha’ari’a har sauran bangarori na ilmomi na daban.
Ya kara da cewa za a gudanar da gasar ne bisa la’akari da cewa adadin ya kai mutane 3000, amma daga karshe dai wadanda za su kai ga mataki na karshe mutane 63 za su kara da juna.
Daga cikin mutane baki daya, za a fitar da mutane 3 da suka zo matakai na daya da na biyu da na uku, sai kuma sauran 60 duk za a basu kyautuka na girmamawa.
3308355